A haramta haska shirin Big Brother Naija: Kungiyar Arewa sun bukaci gwamnatin Najeriya

A haramta haska shirin Big Brother Naija: Kungiyar Arewa sun bukaci gwamnatin Najeriya

  • Kungiyar matasa a Arewa ta yi kira ga gwamnati da babban murya
  • Shirin BBNaija wani shiri ne da ake tara gardawa maza da mata ajanabai kulle cikin wani gida na tsawon watanni
  • Ana zabge mutane daya bayan daya har mutumin karshe wanda shi zai lashe kyautar kimanin milyan 60m

Wata kungiyar bada shawara ta matasa a Arewacin Najeriya (AYCF), ta yi ga gwamnatin tarayya ta haramta haska shirin BBNaija da akeyi a tauraron DSTV.

Shugaban AYCF, Yerima Shettima, ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Juma'a, PT ta ruwaito Daily Trust.

Ya siffanta wannan shiri a matsayin Fitina ga al'umma.

Ya ce bai kamata gwamnati ta bari ana haska irin wannan shiri ba saboda yana koyar da badala da bayyana tsiraici.

Yace:

"Wannan a gani na fitina ne; bana son BBNaija kuma ban tunanin ya dace saboda rashin tarbiyya ne. Bai kamata ana goya bayan irin wannan ba."

Kara karanta wannan

Yadda na tsallake yunkurin kashe ni sau biyu - Kakakin IBB Afegbua

"Na dade ina fadi ya kamata gwamnatin Najeriya ta haramta, bai kamata ana haskawa a kasarmu ba."
"Kun ga, mutane da yawa na kallo don su ga tsiraici."

A haramta haska shirin Big Brother Naija: Kungiyar Arewa sun bukaci gwamnatin Najeriya
A haramta haska shirin Big Brother Naija: Kungiyar Arewa sun bukaci gwamnatin Najeriya Hoto: DSTV
Asali: UGC

An dade ana kira ga gwamnati ta haramta

Wannan ba shi bane karo na farko da za'a yi kira ga gwamnati ta haramta haska BBNaija ba.

Kungiyar kare hakkin Musulmai (MURIC), Kungiyar cigaban jama'a, gidauniyar raya al'adar Afrika da kungiyar iyaye mata, a baya sun bukaci haramta haska wannan shiri.

Wadannan kungiyoyin sun shigar da Kamfanin MutiChoice Nigeria Limited, Hukumar lura da ayyukan gidajen talabijin da rediyo NBC, da gwamnatin tarayya babban kotun tarayya dake Legas.

Bayan haka, Babban Faston Anglican Church of the Epiphany, Ifeanyi Akunna, shima ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta haramta shirin BBNaija da ire-irensa a Najeriya.

Ya ce cigaba da haska wannan shirin zai gurbata tarbiyyan matasan Najeriya.

Arewa maso gabashin Nigeria na iya fuskantar matsanancin Fari da yunwa, UN

Kara karanta wannan

A karshe IBB ya bayyana yadda aka yi masa lakabi da ‘mugun gwani’ da Maradona

A wani labarin kuwa, akalla mutane milyan hudu da rabi a Arewa maso gabashin Nijeria na gabar fuskantar kalubalen rashin abinci, a cewar majalisar dinkin duniya.

A wani jawabi da ofishin kodinatan bada agaji na majalisar ya saki ranar Alhamis, abin ya tsananta a arewa maso gabashin kasar, rahoton AriseNews.

Idan ba agaji aka kaiwa jihohi irinsu Borno, Adamawa da Yobe ba, to mutane zasu sha wahala wurin neman abinda zasu ciyar da kansu a wannan yanayin ha'ulai na shekarar 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel