Siyasa Ta Dauki Zafi: Majalisar Kansiloli Ta Tsige Shugaban Karamar Hukuma a Jihar Neja

Siyasa Ta Dauki Zafi: Majalisar Kansiloli Ta Tsige Shugaban Karamar Hukuma a Jihar Neja

  • Kansiloli a karamar hukumar Chanchaga sun dakatar da ciyaman, Aminu Ladan bisa zargin take doka da kin bin ka’idojin shugabanci
  • Dakatarwar na zuwa ne bayan Aminu ya maka gwamnatin Neja a kotu kan batun wa’adin mulki da kuma kudin kananan hukumomi
  • Ana zargin Aminu da karkatar da kadarori, sayar da filaye ba bisa ka’ida ba, da kuma rashin gabatar da rahoton kudi ga majalisar kansiloli

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Majalisar kansiloli a karamar hukumar Chanchaga da ke jihar Neja, sun kada kuri'ar dakatar da shugaban karamar hukumar, Aminu Ladan.

Kansilolin sun dakatar da Aminu Ladan daga ofishinsa ne bisa zarge-zargen take dokokin gudanarwar aiki da kuma rashin da'a.

Kansiloli sun dakatar da shugaban karamar da ya kai karar Gwamna Umaru Bago a Neja
Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago a ranar da ya rattaba hannu kan wasu dokoki a Nuwambar 2023. Hoto: @HonBago
Source: Twitter

Chanchaga: Kansiloli sun dakatar da ciyaman a Neja

An dakatar da shugaban karamar hukumar ne a ranar Litinin, bayan kansiloli takwas cikin 10 da ke a majalisar kansilolin sun sanya hannu kan kudurin, inji rahoton Sahara Reporters.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An kama bindigogi ana kokarin kai su Kano daga Filato

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Ibrahim Isah Gommna (gundumar Minna ta Kudu) da Mohammmed Mohammed (gundumar Nasarawa) sun ki sanya hannu kan kudurin.

Dakatar da Aminu Ladan na zuwa ne kasa da mako guda da shugaban karamar hukumar ya shigar da karar gwamnatin jihar Neja da wasu mutum hudu a babbar kotun tarayya, Abuja.

Mun ruwaito cewa, Aminu ya bukaci kotu ta tilasta aiwatar da hukuncin Kotun Koli kan turawa kananan hukumomi kudinsu da kuma batun wa'adin ciyamomi da kansiloli.

A lokacin da aka gabatar da karar a Juma'ar da ta gabata, an mika ta ga babban alkalin Najeriya (CJN) domin a mikawa alkalin da zai saurari shari'ar.

Neja: Zarge-zargen da ake yiwa ciyaman

A cikin takardar dakatarwar da jaridar Vanguard ta samu a Minna, kansilolin sun zargi Aminu Ladan da aikata rashin da'a, karkatar da kadarorin karamar hukumar.

Hakazalika, kansilolin sun zargi shugaban karamar hukumar da kin gabatar da takardun kudaden da aka samu da yadda aka kashe su ga majalisar, kamar yadda doka ta tanada.

Kara karanta wannan

Rigima ta barke tsakanin limamai da ƴan addinin gargajiya kan birne Sarki

Sauran zarge-zargen sun hada da kin bin doka wajen sayar da filaye a karamar hukumar, bayar da kwangiloli ba bisa ka'ida ba, rashin iya aiki, kin bin dokoki da kuma kin kafa kwamitin kudi da sauran ayyuka, wani muhimmin kwamiti a gudanarwar karamar hukuma.

Kansilolin sun ce sun sanar da majalisar dokokin jihar Neja game da dakatar da shugaban karamar hukumar da suka yi.
Abdulmalik Sarkindaji, kakakin majalisar dokokin jihar Neja yana jawabi ga wani taro. Hoto: @NupeMufasa
Source: Facebook

An ba ciyaman kwana 5 ya kare kansa

Kansilolin sun bayyana cewa sun sanar da majalisar dokokin jihar Neja game da wannan mataki da suka dauka.

Bugu-da-kari, sun bai wa dakataccen shugaban karamar hukumar wa'adin kwanaki biyar ya yi bayani a rubuce game da zarge-zargen da ake yi masa.

Duk wani kokari na jin ta bakin Aminu Ladan game da lamarin ya ci tura yayin da aka gaza samunsa ta wayar tarho, har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto.

An tsige shugabannin kananan hukumomi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ana ci gaba da tsige shugabannin kananan hukumomi a jihar Edo, bayan majalisun kansiloli sun tsige karin ciyamomi biyu.

Majalisar karamar hukumar Esan Arewa maso Gabas da ta Akoko-Edo ne suka sauke shugabanninsu bisa zargin saba wa ka’idojin shugabanci.

Sai dai ciyamomin da abin ya shafa sun kalubalanci matakin, inda suka ce abin da aka yi ba bisa doka ba ne kuma ba zai dore ba, saboda ya ci karo da kundin tsarin mulki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com