2027: APC Ta Tsorata da Ake Shirin Kawo Sauyi kan Zaben Shugaban Kasa, Gwamnoni
- Manyan jam’iyyun adawa sun goyi bayan gyaran kundin tsarin mulki don gudanar da zabukan 2027 duka a rana daya
- APC da wasu 'yan majalisa sun nuna rashin goyon baya, suna cewa hakan zai haifar da cikas da matsin lamba ga INEC
- Masana shari’a da kungiyoyin farar hula sun bayyana ra’ayoyi mabambanta, wasu na ganin zai rage kashe kudi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Wani gagarumin rikicin siyasa ya taso kan sabon shirin sauya kundin tsarin mulki domin gudanar da zabuka a rana daya a 2027.
Yayin da manyan jam’iyyun adawa kamar PDP, LP, ADC da NNPP suka goyi bayan shirin, APC ta yi watsi da shi da gargadi mai tsanani.

Source: Facebook
Mahangar jam'iyyun adawa kan sauyi a zabe
Wannan shiri, wanda kwamitin Majalisar Wakilai kan sauya kundin tsarin mulki ke jagoranta karkashin Benjamin Kalu, yana cikin yunkurin gyaran dokoki, cewar Punch.
Idan aka amince, INEC za ta gudanar da zaben shugaban kasa, gwamnoni, majalisar tarayya da jiha duka a rana guda domin rage kashe kudade.
Ladipo Johnson na NNPP ya ce:
“Kudin zabe ya yi yawa kamar na gwamnati, duk wata hanya da za ta rage kudi ya kamata a dubata.
“Idan za su yi magudi, za su yi. Amma gudanar da zabe a rana daya zai saukaka tsaro da aiki.”
Haka ma jam'iyyar LP ta ba da goyon baya gaba daya, Obiora Ifoh ya ce hakan zai hana zabuka na wucin gadi da kuma rage tasirin sakamako na baya.
Ya kara da cewa:
"LP na tare da matsayar a yi duka zabuka a rana daya, hakan zai rage kashe kudin tafiyar da zabe da jigilar kayayyaki.”
Shi ma Timothy Osadolor na PDP ya ce:
“Wannan ci gaba ne idan aka yi da gaskiya da niyya. Kudin da ake kashewa kan zabe ya yi yawa.

Kara karanta wannan
Dattijon Arewa ya hararo babban rikici a Najeriya idan aka yi magudi a zaben 2027
“Ba a da wani dalili mai karfi da ya sa gwamnati ke kashe biliyoyin daloli kan zabuka da ba sa kawo ingantaccen sakamako.”

Source: Twitter
Zaben 2027: Matsayar APC da wasu yan majalisa
Har ila yau, jam'iyyar ADC ta bayyana ra'ayinta kan sauyin da ake son kawo wa domin gudanar da zaben 2027, cewar The Nation.
Bolaji Abdullahi na ADC ya ce:
“Goyon bayanmu yana bisa sharadin INEC ta gyara dabarunta. A yanzu ba mu ga hakan daga gare su ba.”
Wasu ‘yan majalisar wakilai sun goyi baya, kamar Sada Soli na APC daga Katsina da ya ce wannan ra’ayi ne “wanda lokacinsa ya yi.”
Sai dai Oluwole Oke daga Osun ya ce:
"INEC ce ke da hurumin yanke ranar gudanar da zabe, ba wai a tilasta mata ba.”
Babajimi Benson daga Lagos ya ce:
“Ya kamata a saka wannan sauyi cikin dokar INEC don a saukaka gyare-gyare, ba a kundin tsarin mulki ba.”
APC ta bayyana adawa da shirin, Nze Chidi Duru ya ce gudanar da duka zabuka a rana daya zai yi wa INEC nauyi da matsin lamba.
Ya ce:
'Dan majalisa, Amobi Ogah ya ce ma’aikata na ci gaba da wulakanta makarantun da asibitocin gwamnati da ke Najeriya.i aiki ba.”
Za a hana jami'an gwamnati jinya a ketare
Mun ba ku labarin cewa majalisar wakilai ta fara duba dokar hana ma’aikatan gwamnati da iyalansu zuwa makarantu da asibitocin kuɗi.
Dan majalisa, Amobi Ogah ya ce ma’aikata na ci gaba da wulakanta makarantun da asibitocin gwamnati da ke Najeriya.
Ya bayyana cewa 'yan 'kasar nan sun kashe Dala biliyan 29.29 don jinya a 'kasashen waje tsakanin 2015 zuwa 2023.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

