'Yan Zamfara Sun Huro Wuta, Suna So Dauda Lawal Ya Sauka daga Kujerar Gwamna

'Yan Zamfara Sun Huro Wuta, Suna So Dauda Lawal Ya Sauka daga Kujerar Gwamna

  • Kungiyar ZGGF ta bukaci Gwamna Dauda Lawal ya gaggauta yin murabus, tana zarginsa da gazawa wajen yaki da ‘yan bindiga
  • Rahotanni sun nuna cewa duk da biyan N50m, ‘yan bindiga sun kashe mutum 35 daga cikin 53 da suka sace a kauyen Banga
  • ZGGF ta roki Shugaba Bola Tinubu ya dauki matakin gaggawa a Zamfara tare da aika karin sojoji don dawo da tsaro a yankunan karkara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Wata kungiya da ke fafutukar mulki na-gari a Zamfara (ZGGF) ta bukaci Gwamna Dauda Lawal da ya yi murabus daga kujerarsa, tana zarginsa da rashin kwarewar shugabanci.

A cewar kungiyar, sauya shugabanci zai iya kawo sabon jini da tsari a yunkurin kawo karshen ‘yan bindiga a jihar Zamfara.

An bukaci Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara da ya yi murabus kan tabarbarewar tsaro
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal a wani taron majalisar tsaro da ya jagoranta. Hoto: @daudalawal_/X
Source: Twitter

An kashe mutane 35 a jihar Zamfara

Kara karanta wannan

Jirgin ƙasa dauke da fasinjoji 100 ya yi hatsari yana cikin gudu, an rasa rayuka

Wannan kiran na zuwa ne bayan kashe mutane 35 daga cikin wadanda aka sace a karamar hukumar Kaura Namoda, duk da an biya kudin fansa na N50m, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, shugaban ZGGF, Alhaji Sani Mohammed, ya bayyana cewa mutanen da aka kashe 'yan kauyen Banga ne.

Ya ce suna daga cikin mutane 53 da aka sace watannin da suka gabata, inda masu garkuwar suka bukaci N1m matsayin kudin fansar kowanne.

Daga cikin kudin da al’ummar suka hada, an biya N50m, amma bayan haka, mutane 18 ne kacal aka sako, sauran 35 kuwa an ce an kashe su, kamar yadda muka ruwaito.

“Abin da ya faru a kauyen Banga babbar musifa ce ga kasa baki daya. An yanka mutane 35 kamar dabbobi duk da an biya kudin fansa.
“Gwamnan da ya yi rantsuwa zai kare rayuka da dukiyoyin jama’a yanzu yana ta wasa da ‘yan ta’adda kamar wasan mage da bera."

- Alhaji Sani Mohammed.

An roki Tinubu ya kai dauki Zamfara

ZGGF ta roki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya ayyana dokar ta baci kan tsaro a Zamfara tare da tura karin sojoji domin dawo da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

An harbe 'dan bindiga ‘Dan Dari Biyar' da ya shahara da gallazawa Hausawa

“Zamfara tana zubar da jini. Matsalar da ke faruwa na bukatar daukar mataki na musamman ba wai wanda aka saba da shi ba. Mutane na da ‘yancin rayuwa cikin mutunci da kwanciyar hankali,” in ji sanarwar.

Kungiyar ta ce al’ummomin karkara da dama a jihar Zamfara sun kara zama cikin hadari, inda ‘yan bindiga ke karbar haraji, yin garkuwa da mutane da kuma mamaye wasu yankuna.

Kungiyar ZGGF ta zargi Gwamna Dauda Lawal da gazawa wajen kawo karshen 'yan bindiga a Zamfara
Dauda Lawa, gwamnan jihar Zamfara yana jawabi a wani taro. Hoto: @daudalawal_/X
Source: Facebook

An nemi Gwamna Dauda ya yi murabus

Jaridar Daily Post ta rahoto kungiyar ZGGF ta bayyana cewa tsarin tsaron Gwamna Lawal cike yake da rudani, rashin daidaito da shisshigi na siyasa.

Kungiyar ta kara da cewa Lawal, wanda ya caccaki Gwamna Bello Matawalle a baya kan gazawar tsaro, yanzu ya nuna gazawa sosai fiye da Matawalle.

“Wannan ba siyasa ba ce, magana ce kan rayuwa ko mutuwa. Ya gaza. Shi kansa ya san da hakan. Kowa ya sani. Cigaba da zama a ofis tamkar cin mutunci ne ga mutanen Zamfara. Ya kamata ya yi murabus cikin mutunci."

- Alhaji Sani Mohammed.

Zamfara: 'Yan bindiga sun kashe mutane 38

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kashe wasu daga cikin sama da mutane 50 da suka sace a jihar Zamfara, Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnonin 1999 sun nemi Tinubu ya ajiye raba tallafi, ya samar da ayyuka ga matasa

Rahotanni sun tabbatar da cewa an hallaka mutum 38 daga cikin waɗanda aka sace a kauyen Banga da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda, duk da an biya kudin fansa.

Aminu Musa Banga ya bayyana cewa 'yan bindigar sun kashe mutanen ne bayan karɓar kuɗin, inda mutum 18 kawai suka tsira kuma aka sako su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com