'Dan Majalisar Kano Ya Gwangwaje Ƴan Mazaɓarsa, Mutum 120 Za Su Ƙaro Karatu
- Ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Bichi, Abubakar Kabir Bichi ya ce ilimi ne hanyar kuɓutar da al’umma daga jahilci
- Saboda haka ne a cewarsa, zai ci gaba da ɗaukar nauyin marasa galihu a mazaɓarsa domin ƙaro karatu a ciki da wajen Najeriya
- A faɗi haka ne a yayin taron ɗaukar nauyin dalibai sama da 120 a fannoni daban- daban a matakin digiri na biyu da na uku
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Bichi a jihar Kano, Abubakar Kabir Bichi, ya sake waiwayar jama'arsa.
A wannan karon, ya biya kuɗin makarantar ɗalibai 121 ‘yan asalin ƙaramar hukumar Bichi da ke karatu a matakin digiri na biyu da digiri na uku wato PhD.

Kara karanta wannan
Yobe: Wata mata, Hadiza Mamuda ta kashe mijinta kan abin da yake kawo mata kullum

Source: Facebook
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa wannan shi ne karo na uku da Kabir-Bichi ke ɗaukar nauyin irin wannan tallafin karatu ga ‘yan mazaɓarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗan majalisar Kano ya bayyana muhimmancin ilimi
A wajen bikin raba tallafin da aka gudanar a Kano a ranar Lahadi, Abubakar Kabir-Bichi ya ce zai ci gaba da tallafawa marasa galihu a matakai daban-daban na ilimi a mazabarsa.
A wata hira da Legit Hausa ta yi da mashawarcin ɗan majalisar kan harkar tallafin karatu, Mukhtar Nura Bichi, ya bayyana cewa ilimi hanya ne na magance jahilci.

Source: Facebook
Ya ce ɗan majalisar na ci gaba da ɗaukan nauyin karatun ƴan mazaɓarsa a ciki da wajen Najeriya.
Ya ce:
“Kamar yanzu akwai kwasa-kwasai da ba sai mutum ya fita ƙasashen waje ba, irinsu Hausa. Amma su waɗanda suke fita waje, sune sababbin kwasa-kwasai kuma suna da wahala, kuma wasu jami'o’in ba su da isassun kayan koyar da su.”

Kara karanta wannan
Gaskiya ta fito: An ji dalilan da suka jawo naɗa Ministan Tinubu a matsayin shugaban APC
Ɗan majalisar ya kai ɗalibai makarantun Najeriya
Waɗanda suka amfana da tallafin sun fito ne daga jami’o’i daban-daban da ke fadin Najeriya, bayan tantance su da kwamitin ilimi ƙarƙashin Dr. Habibu Usman-Abdu.
Daliban da yawan jami'o'in da suka amfana sun haɗa da: Jami’ar Bayero Kano mutum 58, dalibai 24 daga jami’ar tarayya Dutsin-Ma, da Jami’ar Northwest a Kano mutum takwas.
Sai jami’ar Fasaha ta Aliko Dangote da ɗalibai bakwai, jami’ar Ahmadu Bello, Zariya mutum bakwai da jami’ar fasaha ta tarayya, Minna mai dalibai hudu.
Sauran su ne dalibai biyu Daga jami’ar tarayya Dutse, jami’ar Abubakar Tafawa Balewa mutum biyu da jami’ar Jos mutum ɗaya.
Sai kuma jami’ar Najeriya, Nsukka mutum daya, jami’ar Jihar Nasarawa, Keffi mutum biyu da kuma NDA Kaduna mutum biyu.
Taron raba tallafin ya samu halartar wakilan jami’o’in da aka ambata, ma’aikatan ofishin dan majalisa, shugabannin al’umma da kungiyoyin dalibai.
Ɗan majalisar Kano ya ɗauki nauyin ɗalibai
A baya, mun wallafa cewa Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Bichi a Kano, Hon. Abubakar Kabir Bichi, ya buɗe sabon zagaye na ɗaukar nauyin karatun dalibai mata.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Abba ta dura kan bangaren lafiya, za a gyara asibitoci sama da 200 a faɗin Kano
Wannan na zuwa ne ƙarƙashin shirin tallafin karatu na kasashen waje da ofishin mai ba shi shawara na musamman ke gudanarwa don taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi.
Ya bayyana cewa daliban za su yi karatu ne a fannonin kimiyya da fasaha da suka shafi ci gaban rayuwa, waɗanda ke da wahalar samu a cikin Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng