Tashin Hankali: Saurayi Ya Sari Tsohuwar Budurwarsa da Adda, Ya Kashe Mahaifiyarta

Tashin Hankali: Saurayi Ya Sari Tsohuwar Budurwarsa da Adda, Ya Kashe Mahaifiyarta

  • Ana zargin wani matashi mai suna Abubakar Ijidai ya farmaki tsohuwar budurwarsa da mahaifiyarta, inda ya sassare su da adda
  • Lamarin ya faru ne da misalin karfe uku na rana a gundumar Dille, da ke jihar Borno, inda ya kashe mahaifiyar budurwar nan take
  • Jami’an ‘yan sanda daga ofishin Lassa sun kai dauki, inda aka tabbatar da mutuwar Hauwa Azuba, aka kuma mika budurwar asibitin Mubi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Al'ummar gundumar Dille da ke karamar hukumar Askira/Uba ta jihar Borno sun tashi da wani mummunan lamari a ranar Asabar, 26 ga Yulin 2025.

An rahoto cewa wani matashi, Abubakar Ijidai ya farmaki tsohohuwar budurwarsa da mahaifiyarta yayin da suke aiki a cikin gona.

Wani matashi ya kashe mahaifiyar tsohuwar budurwarsa, ya raunata budurwar a Borno
Sabon kwamishinan 'yan sandan jihar Borno, CP Naziru Abdulmajid. Hoto: @BornoPoliceNG
Source: Twitter

Saurayi ya kashe mahaifiyar tsohuwar budurwarsa

Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ya rahoto a shafinsa na X cewa ana zargin Abubakar Ijidai ya yi sassari budurwar da adda, sannan ya kashe mahaifiyarta.

Kara karanta wannan

Musulunci ya yi babban rashi, Sheikh Dalha Konduga ya rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce dai wannan mummunan lamari ya faru ne da misalin karfe 3:00 na rana, kuma abin ya shafi wata Lami, 'yar shekara 18 da mahaifiyarta Hauwa Azuba, 'yar shekara 38.

Tsohon saurayin Lami, watau Abubakar ya dauki adda ya bi sahun matan har cikin gona, inda ya farmake su da sara, kamar yadda rahoton ya nuna.

Majiyoyi sun shaida cewa wanda ake zargin, ya kasance dan asalin wannan gundumar ne, kuma ya tsere bayan ganin irin aika-aikar da ya yi.

An kai tsohuwar budurwar asibitin Mubi

A cewar majiyoyin, jami'ai daga ofishin 'yan sanda na Lassa sun ziyarci wurin da abin ya faru, kuma sun dauki wadanda abin ya shafa zuwa asibitin Lassa.

Wata majiya ta ce:

"Sai dai abin takaici, likitan da ya duba matan ya tabbatar da mutuwar Hauwa Azuba, yayin da 'yarta Lami, aka mayar da ita babban asibitin Mubi da ke jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Ginin makaranta ya rufta kan dalibai suna tsakiyar karatu, an samu asarar rayuka

"Ana sa ran likitocin asibitin Mubi za su ci gaba da kula da ita, la'akari da irin mummunan raunukan da ta samu daga harin."
'Yan sanda na gudanar da bincike yayin da wani matashi ya kashe mahaifiyar tsohuwar budurwarsa a Borno
Taswirar Najeriya da ke nuna jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan sanda sun fara gudanar da bincike

An rahoto cewa, jami'an tsaro sun dauki hoton gawar Hauwa Azuba domin gudanar da cikakken bincike kan mutuwarta.

Hakazalika, an mika gawarta ga iyalanta da ke gundumar Dille, karamar hukumar Askira/Uba domin su birne ta bisa tsarinsu na addinin Kiristanci.

Shugabannin gundumar sun yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar an nemawa yarinyar adalci.

Rundunar 'yan sanda dai ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, kuma za ta kamo wanda ake zargi domin gurfanar da shi gaban kuliya.

Saurayi ya kashe budurwarsa a Kaduna

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami’an ‘yan sanda a jihar Kaduna sun cafke wani mutumi wanda ake zargin ya kashe buduwarsa, saboda za ta rabu da shi.

An ce 'yan sanda sun isa wurin da abin ya faru, inda suka tarar da wanda ake zargi a kwance zagaye da tulin mutane sun yi masa rotse.

Ana zargin mutumin mai suna Keneth ya sari Ebenezer Agada mai shekara 27 da adda a fuska da hannuwa, kuma ta mutu a asibitin koyon aiki na Barau Dikko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com