Yadda saurayi ya kashe tsohuwar budurwarsa don burge sabuwar budurwa

Yadda saurayi ya kashe tsohuwar budurwarsa don burge sabuwar budurwa

Wani mutum ya kashe tsohuwar budurwarsa domin ya nuna wa sabuwar budurwarsa tsananin kaunar da ya ke mata kamar yadda masu bincike suka fadi a wani rahoto na The Mirror.

Wanda ake zargin, Petrov mai shekara 20 ya tafi da tsohuwar budurwarsa Anastasia Pospelova zuwa daji kafin ya shake mata wuya har sai da ta mutu.

Petrov da sabuwar budurwarsa Yekaterina Karpova mai shekara 20 sun gayyaci Anastasia zuwa wani party a ranar 14 ga watan Yuni. Bayan ta iso wurin taron, masoyan biyu sun kai ta jeji inda suka kunna wuta don shan dumi suna shan giya.

Yadda saurayi ya kashe tsohuwar budurwarsa don birge sabuwar budurwa
Yadda saurayi ya kashe tsohuwar budurwarsa don birge sabuwar budurwa. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

Petrov ya ciro wuka daga aljihunsa ya caka wa Anastasia a wuyanta. Cikin firgici ta yi kokari ta tunkude shi ta tsere jini na zuba daga jikinta.

DUBA WANNAN: Cin amana: Matar aure ta yiwa mazakutar mijinta 'mugun riko' har ya fadi sumamme

Ta kira wata kawarta tana neman a kawo mata taimako yayin da ta boye a daji, amma kawar sai ta yi tsamanin ba a ne ta ke mata sakamakon giya da ta sha.

Bayan ta yi wannan kirar wayan, Petrov ya gano inda ta ke ya kuma sake kai mata hari.

Wannan karon Petrov ya caka mata wukar a kirji kafin ya take wuyanta har sai da ta mutu. Sannan shi da sabuwar budurwarsa Karpova suka boye gawar a cikin daji sannan suka koma kauyen suka ce Anastasia ta bace.

Daga bisani, yan sanda sun gano gawar tsohuwar budurwar tare da alamun wahalar da ta sha kafin a kashe ta.

Yayin bincike, Karpova da Petrov sun amsa cewa su suka aikata laifin in ji yan sanda.

Masu bincike sun ce Karpova wace ke da yaro mai shekaru biyu tana kishin irin soyayyar da Petrov da Anastasia suka yi ne kuma ta kan taso da maganan a lokuta daban daban.

Hakan yasa Petrov ya amince zai kashe Anastasia domin ya nuna kaunarsa ga Karpova kuma su dena samun sabani a kan lamarin.

A cewar masu binciken, "Wanda ake zargin ya caka wa marigayiyar wuka sannan ya take mata wuya har ta mutu. Wadanda ake zargin sun kai karar cewa marigayiyar ta bata don kada a zarge su.

"Bayan an gano gawarta sun amsa cewa sune suka aikata laifin. Za su fuskanci daurin shekaru 15 a gidan yari idan aka tabbatar da laifin da ake zarginsu da aikatawa."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel