Belin Dilan Ƙwaya: Gwamna Abba Kabir Ya Kafa Kwamiti game da Kwamishinansa a Kano

Belin Dilan Ƙwaya: Gwamna Abba Kabir Ya Kafa Kwamiti game da Kwamishinansa a Kano

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamiti domin bincikar rawar da Kwamishinan Sufuri ya taka wajen belin wani da ake zargin da safarar kwaya
  • Sunan Kwamishinan ya bayyana a takardun da suka taimaka wajen sakin wanda ake zargin, abin da ya jawo Allah wadai a ciki da wajen Kano
  • Abba ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci laifi ko ɗaukar nauyin masu safarar miyagun ƙwayoyi ba, kwamiti zai binciki Ibrahim Namadi Dala

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya dauki mataki mai tsauri domin yaki da safarar kwayoyi a jihar.

Abba Kabir ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan rawar da Kwamishinan Sufuri, Alhaji Ibrahim Namadi, ya taka a belin wani da ake zargi.

Abba Kabir ya kafa kwamitin binciken kwamishinansa
Abba Kabir ya kafa kwamiti game da kwamishinansa a Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Za a binciki hannun kwamishina a belin dan kwaya

Kara karanta wannan

Babbar magana: An yi barazanar kama gwamnan babban bankin Najeriya, CBN

Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature D/Tofa ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan umarni ya biyo bayan zarge-zargen da ke cewa sunan Kwamishinan ya fito a cikin takardun belin wani da ake zargin da safarar miyagun ƙwayoyi.

An sako wanda ake zargin mai suna Sulaiman Aminu Dan Wawu bisa wasu takardu da ke ɗauke da sunan Kwamishinan, lamarin da ya tayar da kura.

Zargin safarar kwaya: Yadda NDLEA ta kama matashi

A watan Mayun 2025 ne Hukumar NDLEA ta shigar da kara kan matashin a gaban kotun tarayya a Kano kan tuhumar safarar miyagun kwayoyi.

Ana zargin an kama matashin da miyagun kwayoyi da suka hada da Tramadol, Rohypnol da Pregabalin, dukkaninsu na kamanceceniya da hodar iblis.

NDLEA ta ce ta kuma bayyana cewa ana yiwa Sulaiman Danwuwu tuhume-tuhume takwas, dukkaninsu a kan safarar kwayoyi masu hadari.

Abba Kabir ya sha alwashin yaki da safarar kwayoyi
Abba Kabir ya kafa kwamiti game da kwamishinansa a Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Abba ya kafa kwamitin binciken kwamishinansa

Gwamna Abba Kabir ya kafa wani kwamiti na musamman domin bincikar lamarin, karkashin jagorancin Barista Aminu Hussain, mai ba shi shawara kan harkokin shari’a.

Kara karanta wannan

Gwamnonin da suka hana Peter Obi, Wike ziyartar jihohinsu a 2025

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Barista Hamza Haladu, Barista Hamza Nuhu Dantani, Alhaji Abdullahi Mahmoud Umar da Manjo-Janar Sani Muhammad mai ritaya.

Haka kuma akwai Kwamred Kabiru Said Dakata da Hajiya Bilkisu Maimota wacce za ta kasance sakatariyar kwamitin binciken da aka kafa.

Sanarwar ta ce kwamitin zai gabatar da rahoto cikin gaggawa tare da shawarwarin da suka dace.

Gwamna Yusuf ya nuna damuwa kan lamarin, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa na fafutukar dakile safarar miyagun ƙwayoyi da sauran laifuffuka.

Ya ce duk wani jami’i da aka samu da hannu cikin irin wannan laifi ba zai samu kariya daga gwamnati ba, kuma za a ɗauki mataki.

Abba Kabir zai gyara asibitoci fiye da 200

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Kano ta ayyana shirin fara gyara cibiyoyin lafiya 203 a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.

Sanarwar da Ibrahim Adam, hadimin gwamnan Abba Kabir Yusuf ya fitar ta ce tuni aka fara aikin a ƙaramar hukumar Bichi.

Malam Ibrahim ya kara da cewa matakin na ƙara nuni ga kudurin gwamnatin Kano wajen fara aikin nan da gaggawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.