Dangote Ya Yi Murabus daga Shugabancin Kamfaninsa, Ya Faɗi Inda Zai Maida Hankali
- Alhaji Aliko Dangote ya yi murabus daga shugabancin kamfaninsa na siminti domin mayar da hankali wani bangare
- Dangote ya ajiye aikin ne a ɓangaren sminiti don mayar da hankali kan matatar mai, sinadarai da hulda da gwamnati
- Emmanuel Ikazoboh zai maye gurbin Dangote a matsayin sabon shugaban kamfanin, yayin da Hajiya Mariya Dangote ta shiga kwamitin kamfanin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Kamfanin Dangote ya tabbatar da murabus din shugabansa na sashen siminti, Alhaji Aliko Dangote.
Kamfanin simintin ya ce Aliko Dangote, wanda shi ne mai hannun jari mafi girma kuma wanda ya kafa kamfanin, ya ajiye aiki.

Source: Getty Images
Dangote ya yi murabus daga kamfanin siminti
Hakan na cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulda da jama’a na Dangote Anthony Chiejina ya fitar, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Chiejina ya ce Dangote ya bar mukamin ne don maida hankali kan bangaren kamfanin matatar mai.
Ya ce zai fi mayar da hankali ne kan matatar mai ta Dangote, kamfanin sinadarai da na takin zamani, da kuma hulda da gwamnati.
An naɗa wanda zai maye gurbin Dangote?
Chiejina ya bayyana cewa Emmanuel Ikazoboh, wanda ya kasance mamba mai zaman kansa a kwamitin kamfanin, shi ne aka nada sabon shugaban kamfanin.
Hakazalika, mai magana da yawun kamfanin ya ce an nada Hajiya Mariya Aliko Dangote a kwamitin, yayin da Dorothy Ufot ta yi ritaya.
Ya ce:
“Shahararren ɗan kasuwa kuma wanda ya kafa 'Dangote Cement Plc', Aliko Dangote, ya sanar da murabus dinsa daga shugabancin kamfanin.
“Ya bar mukaminsa ne don maida hankali kan matatar mai, sinadarai, takin zamani da hulda da gwamnati don cimma burin kasuwanci na shekaru 5.
“Kwamitin simintin Dangote ya sanar da nadin Emmanuel Ikazoboh a matsayin sabon shugaban kamfanin. Haka kuma an nada Hajiya Mariya a kwamitin.

Source: UGC
Gudunmawar da Aliko Dangote ya ba kamfanin
Chiejina ya ce Aliko Dangote ya ba da gudunmawa a masana'antar, inda hangen nesansa ya sauya harkar siminti a Najeriya da Nahiyar Afirka baki ɗaya, Punch ta ruwaito.
“Dangote ya fara ne da burin samar da isasshen siminti a Najeriya da Afirka. Ya cika burin, har ma ya wuce shi.
“Kamfanin simintin Dangote na da ƙarfin sarrafa tan miliyan 52 a Afirka gaba ɗaya, inda Najeriya ke da tan miliyan 35.25.
“An fara gina sababbin masana’antu a Cote d’Ivoire da Itori, Nigeria. Idan sun kammala, ƙarfin zai kai tan miliyan 61.
“A ƙarƙashin jagorancinsa, kamfanin ya samu mafi yawan kuɗin shiga da ribar EBITDA a tarihinsa."
- Inji Chiejina
Dangote ya yi murabus daga kamfanin sukari
Kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya ajiye aiki a matsayin shugaban hukumar kamfanin sukari na Dangote bayan shafe shekaru 20 yana jagoranci.

Kara karanta wannan
Cacar baki ta kaure tsakanin Akpabio da Barau da aka zo tantance wani tsohon sanata
Kamfanin ya ce Dangote ya jagoranci manyan ayyuka a jihohin Adamawa, Taraba da Nasarawa don karfafa samar da sukari a gida da rage shigo da kaya.
Tsohon shugaban bankin Ecobank, Arnold Ekpe ya gaji kujerar Dangote a matsayin sabon shugaban, bayan cikakken tsarin tantancewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

