'Yan Siyasa, Sarakuna da Manyan da ba Su Halarci Jana'izar Buhari ba a Daura

'Yan Siyasa, Sarakuna da Manyan da ba Su Halarci Jana'izar Buhari ba a Daura

A ranar Lahadi 13 ga watan Yulin 2025 aka sanar da rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari bayan fama da jinya na tsawon lokaci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

An tabbatar da rasuwar marigayin a yammacin ranar a birnin London da ke kasar Birtaniya bayan shafe kwanaki yana jinya.

Tinubu ya karrama Buhari bayan rasuwarsa
Manyan mutane da ba je jana'izar Buhari ba. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Muhammadu Buhari.
Source: Twitter

Abin da Tinubu ya yi bayan rasuwar Buhari

Sanarwar da hadimin shugaban kasa ya fitar a shafin X ta ce Tinubu ya umarci matakinsa, Kashim Shettima zuwa London.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya bukaci Shettima zuwa London ne domin rako gawar tsohon shugaban kasa saboda yi mata sutura.

An gudanar da sallar jana'izar Buhari a ranar Talata 15 ga watan Yulin 2025 a garin Daura da ke jihar Katsina.

Manyan mukarraban gwamnati da gwamnoni da yan siyasa da sarakuna sun samu halartar jana'izar, jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ana kewar Buhari, Tinubu da manyan APC za su yi taron farko na maye gurbin Ganduje

Sai dai akwai manyan yan siyasa da wasu sarakuna da ba su samu halartar jana'izar ba.

Legit Hausa ta duba jerin wadanda ba su samu damar halartar jana'izar Buhari ba.

1. Rabi'u Musa Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bai samu damar halartar jana'izar ba.

Mutane da dama sun yi ta maganganu kan rashin zuwan Kwankwaso inda suke zargin bambancin siyasa ne sanadi.

Sai dai daga baya, Kwankwaso ya tafi har zuwa garin Daura domin mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayi.

An soki kwankwaso saboda kin halartar jana'izar Buhari
Kwankwaso ya yi ta'aziyya bayan rasuwar Buhari a Daura. Hoto: Muhammadu Buhari, Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Twitter

2. Abdullahi Umar Ganduje

Shi ma tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje bai samu damar halartar jana'izar Buhari ba saboda wasu dalilai.

Sai dai hadiminsa na musamman ya fayyace dalilin da ya sa bai je jana'izar ba inda ya gargadi mutane kan yada abin da ba su da tabbaci a kai.

Ya tabbatar da cewa Ganduje yana birnin London ne a lokacin da marigayin ya rasu da kuma dawo da shi Daura.

Martanin Ganduje ya ɗan kwantar da hankula bayan jana'izar Buhari sai dai magana ta taso yayin da ake yada cewa shi ma jinya yake yi a London wanda daga bisani aka ƙaryata labarin.

Kara karanta wannan

UNIMAID: An faɗi babban dalilin da ya sa Tinubu ya sauya sunan jami'a saboda Buhari

Ganduje yana London lokacin da Buhari ya rasu
Ganduje da yan siyasar da ba su je jana'izar Buhari ba. Hoto: All Progressives Congress.
Source: Twitter

3. Malam Ibrahim Shekarau

Har ila yau, mutane sun yi ta maganganu game da rashin ganin fuskar tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau a wurin jana'izar.

Tsohon gwamnan Kano ya mulki jihar daga shekarar 2003 har zuwa 2011 kafin Sanata Rabi'u Kwankwaso ya sake dawowa mulki.

Rashin ganin manyan yan siyasa daga jihar Kano musamman tsofaffin gwamnoni da suka mulki jihar ya sanya shakku a zukatan mutane.

Wasu na ganin hakan bai rasa nasaba da bambance-bambancen siyasa tsakaninsa da Buhari duk da cewa Ganduje dan APC ne.

4. Sarki Muhammadu Sanusi II

Mutane da dama sun yi ta korafi kan rashin ganin Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II yayin jana'izar.

Musabbabin abin da ya fi jan hankalin mutane shi ne ganin Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero yayin jana'izar.

Sai da daga baya makusancin Sanusi II ya bayyana dalilin rashin ganin basaraken a wurin jana'izar.

Sanarwar ta ce Sarki Sanusi yana halartar wani taro ne a birnin London lokacin jana'izar wanda hakan ya hana shi samun damar zuwa Daura.

Kara karanta wannan

Bayan Buhari, Bola Tinubu zai je jihar Kano ta'aziyyar Aminu Dantata

An fadi dalilin rashin ganin Sanusi II a jana'izar Buhari
Sarki Sanusi II bai samu zuwa jana'izar Buhari ba a Daura. Hoto: Sanusi II Dynasty.
Source: Facebook

5. Dauda Kahutu Rarara

Rashin ganin Rarara a wurin jana'izar yafi tayar da kura duba da alakar da ke tsakaninsa da marigayi Buhari yayin mulkinsa.

Mawakin ya rera fitattun wakoki ga Buhari yayin da yake neman takara da kuma bayan ya samu nasara wanda ake daukarsa a matsayin mai gidansa.

Sai dai abin mamaki Rarara bai je jana'izar ba kuma bai yi rubutu na musamman a kafar sadarwa domin yin jaje ba.

Amma bayan wasu kwanaki, Rarara ya wallafa bidiyon da ake birne Buhari da yin addu'o'i ba tare da kiran sunansa ba.

An caccaki Rarara bayan rasuwar Buhari
Rarara bai halarci jana'izar Buhari ba. Hoto: Bashir Ahmad, Dauda Kahutu Rarara.
Source: Facebook

Buhari: Abin da muka sani kan asibitin London

A wani labarin mai kama da wannan, an samu bayanan kan asibitin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasu a London bayan ya kwanta rashin lafiya.

Wasu majiyoyi sun ce marigayin ya rasu ne duk da cewa an shirya sallamarsa ranar Lahadi 13 ga watan Yulin 2025.

Asibitin da Buhari ya mutu ya na cikin mafi tsada a Birtaniya, inda ake biyan har £3,500 (N7m) kullum a dakin ICU.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.