Taron APC: Osinbajo Ya Faɗi Wasu Halayen Buhari da Suka Raunana Zukatan Mutane

Taron APC: Osinbajo Ya Faɗi Wasu Halayen Buhari da Suka Raunana Zukatan Mutane

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya yi magana game da halayen tsohon mai gidansa, Muhammadu Buhari
  • Osinbajo ya yabawa Buhari da cewa ya yi mulki da gaskiya da rikon amana a Najeriya wanda ya kamata a yi koyi da shi
  • Farefsa Osinbajo ya ce Buhari ya bi doka da tsarin mulki, ya fafata sau uku a kotu kafin samun nasara a karo na hudu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, SAN, ya koda marigayi Muhammadu Buhari wanda ya kasance mai gidansa.

Osinbajo ya ce marigayi Buhari ya tabbatar da yiwuwar mulki da gaskiya da adalci da kuma rikon amana a Najeriya.

Osinbajo ya yabawa halayen Buhari
Osinbajo ya faɗi irin yadda Buhari ya mulki Najeriya. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: Facebook

'Buhari ya yi mulki da gaskiya' - Farfesa Osinbajo

Yayin jawabi a taron NEC na APC domin girmama Buhari, Osinbajo ya ce yana tuna halayen kirki na marigayin, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Babu kuɗi': Yadda Buhari ya roƙi gwamnoni su tara N700m kafin ya biya su daga baya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Osinbajo ya ce Buhari ya nuna yadda ake mulki na gaskiya tare da yin adalci da bin doka da oda.

Ya ce:

“A shekarunsa da dama na mulki, Buhari ya nuna ana iya mulki da gaskiya, bayyananniyar doka da kuma rikon amana.”
Osinbaji yana cigaba da cewar Buhari
Farfesa Yemi Osinbajo ya ya yabawa halayen Muhammadu Buhari. Hoto: Professor Yemi Osinbajo.
Source: Twitter

Osinbajo ya fadi kyawawan halayen Buhari

Osinbajo ya kara da cewa, a matsayinsa na dan dimokradiyya na gaskiya ya ce Buhari ya jajirce wajen bin doka, ya tsaya takara har sau uku, ya fadi, amma ya bi hakkinsa a kotu.

“Ya fadi a dukkan lokuta ukun, amma a karo na hudu ya samu nasara. Ya nuna cikakken imani da tsarin mulki da doka.

- Cewar Osinbajo

Tsohon mataimakin shugaban ya samu gayyata zuwa taron NEC na jam’iyyar APC a ranar Alhamis, wanda shi ne na farko tun bayan rasuwar Buhari, cewar Arise News

Shekarun da Osinbajo, Buhari suka yi a mulki

Osinbajo, daya daga cikin wadanda suka kafa APC, ya yi aiki tare da Buhari har na shekaru takwas a lokacin da yake kan karagar mulki.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta ƙara fitowa, an ji babban abin da ya hana Buhari korar wasu ministoci a mulkinsa

Farfesa Osinbajo ya rike mukamin mataimakin shugaban kasa a mulkin marigayi Muhammadu Buhari wanda ya rasu a ranar Lahadi 13 ga watan Yulin 2025.

Ya rike mukamin har na tsawon shekarun daga shekarar 2015 zuwa 2023 bayan samun nasara a zaben da aka gudanar shekaru 10 da suka gabata.

Tinubu da mahalarta taron NEC na APC

Shugaban kasa mai ci, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, da sauran jiga-jigan jam’iyyar sun halarci taron NEC na APC.

Yayin taron ne aka tabbatar da nadin sabon shugaban APC, Yilwatda Nentawe bayan murabus din Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Tinubu ya taya Osinbajo murnar cika shekaru 68

A baya, kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya taya tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, murnar cikarsa shekaru 68, yana yabonsa bisa kokarinsa ga kasa.

Tinubu ya jaddada rawar da Osinbajo ya taka wajen gudanar da gwamnati da ayyukan ci gaba lokacin da yake mataimakin Muhammadu Buhari.

Ya kuma tuna yadda Osinbajo ya nuna kwarewarsa a lokacin da ya zama mukaddashin shugaban kasa yayin da Buhari ke jinya a Birtaniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.