Babu Sauki: Jami'an Tsaro Sun Ragargaji 'Yan Bindiga a Zamfara

Babu Sauki: Jami'an Tsaro Sun Ragargaji 'Yan Bindiga a Zamfara

  • Ƴan bindiga sun ji ba daɗi bayan jami'an tsaro sun shirya musu kwanton ɓauna a jihar Zamfara
  • Jami'an tsaron sun hallaka ƴan bindiga bayan sun yi musu kwanta-kwanta a ƙaramar hukumar Gusau
  • Biyo bayan harin, mutanen ƙauyukan yankin sun bar gidajensu domin gudun ramuwar gayya daga wajen ƴan bindigan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Jami'an tsaro sun hallaka aƙalla mutane biyu da ake zargi ƴan bindiga ne a ƙaramar hukumar Gusau ta jihar Zamfara.

Lamarin ya haifar da ɗimbin gudun hijira daga ƙauyukan da ke kewaye, sakamakon fargabar kai harin ramuwar gayya daga sauran ƴan bindiga.

Jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga a Zamfara
Jami'an tsaro sun hallaka 'yan bindiga a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Jami'an tsaro sun kashe ƴan bindiga

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da wannan lamari a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, 23 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

Zamfara: Mutane sun gaji da hare haren 'yan bindiga, sun nuna fushinsu ga gwamnati

An bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 22 ga watan Yulin 2025, lokacin da wasu maharba daga garin Mada suka shirya kwantan ɓauna kan ƴan bindigan tsakanin ƙauyukan Fegin Mahe, Chuna, Kanawa da Gundumau.

Majiyoyin sun bayyana cewa harin kwantan ɓaunar ya yi sanadiyyar kashe ƴan bindiga biyu, lamarin da ya jefa fargaba cikin mazauna ƙauyukan da abin ya shafa.

Yawancinsu sun tsere zuwa garin Mada don neman mafaka, yayin da wasu kuma suka nufi gidan gwamnatin jihar Zamfara da ke Gusau don yin zanga-zanga suna neman kariya daga yiwuwar harin ramuwar gayya.

Masu zanga-zangar na ɗauke da alluna suna neman ɗaukar matakin gaggawa daga gwamnati da ƙarfafa tsaro a yankin don kare su daga hare-haren ƴan bindiga masu addabar al’umma.

Ƴan sanda za su ɗauki mataki

Da yake mayar da martani kan zanga-zangar, kwamishinan ƴan sanda na jihar Zamfara ya gudanar da wani taron gaggawa da shugabannin al’umma daga yankunan da lamarin ya shafa.

An yi zanga-zanga a jihar Zamfara
'Yan sanda za su tura jami'ai a yankunan Zamfara Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kwamishinan ya tabbatar musu da cewa za a ɗauki matakin gaggawa domin tabbatar da tsaro a yankin.

Ya umurci cewa a raka Dagatan ƙauyukan tare da motar yaƙi mai sulke (APC) a matsayin mataki na wucin gadi, kafin a kammala tura dakarun hadin gwiwa da za su tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki manoma a Zamfara, an rasa rayuka

Yanzu haka, an shawo kan lamarin kuma ana ci gaba da sa ido sosai.

Ƴan bindiga sun farmaki ƙauyuka a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a wasu ƙauyukan jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun kai hare-haren ne a wasu ƙauyuka uku na ƙaramar hukumar Bakura inda suka kashe mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.

A ɗaya daga cikin ƙauyukan, ƴan bindigan sun ritsa wasu manoma da ke aiki a gona inda suka hallaka mutum huɗu har lahira bayan sun buɗe musu wuta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng