'Za Su Iya Tarwatsa Jihar Kano': NAFDAC Ta Ƙwace Sinadaran Haɗa Abubuwan Fashewa
- NAFDAC ta gano sinadaran hada bam a gidan da ke Kwakwachi a Kano, inda aka kama lita 88,560 na sinadarai masu matuƙar haɗari
- Shugabar NAFDAC, Farfesa Mojisola, ta ce adadin sinadaran da aka kama zai iya tarwatsa gaba daya jihar Kano idan aka yi sakaci da su
- An kama manajan gidan, Sani Bala, yayin da ake ci gaba da neman ubangidansa da suka yi shekara biyu suna harkar ba tare da lasisi ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Hukumar NAFDAC ta rufe wani gida a jihar Kano bayan gano tarin sinadarai masu haɗari da ake iya amfani da su wajen hada abubuwan fashewa.
NAFDAC ta gano gidan ne a ranar Laraba a unguwar Kwakwachi da ke karamar hukumar Fagge, bayan samun bayanan sirri da kuma binciken da ta gudanar.

Source: Twitter
An gano gidan ajiyar sinadaran hada bam
An gano cewa gidan na ɗauke da lita 60,000 na sulphuric acid da kuma lita 28,560 na nitric acid, tare da galan-galan 330 da babu komai a ciki, inji rahoton Punch.
Shugabar hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, wadda Dr. Martins Iluyomade ya wakilta, ta bayyana cewa wannan samame “ya firgita ta sosai.”
Farfesa Mojisola ta bayyana cewa wannan shi ne ɗaya daga cikin mafi girman samamen da hukumar ta taba yi kan gidan ajiye haramtattun sinadarai.
A cewar shugabar hukumar NAFDAC:
“Abin da muka gani a nan ya firgita mu; ban taɓa ganin wannan yawan sinadaran nitric da sulphuric acid a wuri guda ba kamar haka.”
"Za su iya tarwatsa jihar Kano" - Mojisola
Farfesa Mojisola ta bayyana cewa mai gidan ba dillalin sinadarai ne da aka yiwa rajista ba, kuma bai mallaki izini ko lasisin da ofishin Malam Nuhu Ribadu (NSA) ke bayarwa ba.

Kara karanta wannan
Ta faru ta kare, majalisa ta amince Tinubu ya kinkimo bashin Naira tiriliyan 32.2
“Mai wannan gidan ba shi cikin jerin dillalan sinadarai da aka amince da su. Muna da kundin da muke amfani da shi wajen sa ido kan shigo da sinadarai, amfani da su da kuma yadda ake zubar da su.
“Waɗannan sinadarai ne masu tsananin bukatar kulawa da ba kowa ke da izinin mu’amala da su ba. Shigo da su ƙasar nan na bukatar takardar izini daga ofishin NSA. Wannan mutum kuwa bai da kowanne daga cikinsu.
“Dalilin da ya sa ake buƙatar lasisi da izini shi ne saboda irin waɗannan sinadarai ana amfani da su ne wajen ƙera bama-bamai.
"Adadin sinadaran da muka kama a wannan gidan kaɗai ya isa ya tarwatsa gaba ɗayan Kano idan aka yi sakaci da su.”

Source: Twitter
NAFDAC ta cafke manajan gidan a Kano
Jaridar The Nation ta rahoto cewa Farfesa Mojisola ta ƙara da cewa bincike na ci gaba da gudana domin gano ainihin mai gidan, wanda a yanzu ya tsere.
“Za mu tabbatar da cewa an kamo shi kuma an gurfanar da shi. Ya kamata ya fadi yadda aka shigo da sinadaran da kuma wa yake sayar mawa. Wannan al’amari babbar barazana ce ga tsaron ƙasa."

Kara karanta wannan
An zargi gwamnati da hannu a watsar da aikin titin Kano zuwa Katsina, ana asarar rayuka
An kuma ruwaito cewa an kama manajan wajen, wani mai suna Alhaji Sani Bala, mai shekara 74. Bala ya bayyana cewa sukan samo sinadaran ne daga jihar Ogun.
Ya shaida wa manema labarai cewa shi da ubangidansa sun shafe shekara biyu suna harkar a unguwar Kwakwaci, ƙarƙashin kamfanin da aka kira “Victor Chidi Ike General Enterprises."
An gano karin ababen fashewa a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta gano bama-bamai tara da ba su fashe ba a kamfanin sarrafa ƙarafa na Yongxing da ke jihar.
Rahoton ya nuna cewa, a ranar Asabar da ta gabata, ɗaya daga cikin bama-baman, nau’in UXO, ya fashe a cikin kamfanin, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane biyar.
Binciken da aka gudanar ya gano cewa an shigo da bama-baman ne a cikin kayan gwan-gwan daga jihar Yobe, ba tare da sanin cewa suna ɗauke da abubuwan fashewa ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
