Garambawul: Gwamna Ya Rantsar da Sababbin Kwamishinoni 6, Ya Sauya Muƙaman Wasu

Garambawul: Gwamna Ya Rantsar da Sababbin Kwamishinoni 6, Ya Sauya Muƙaman Wasu

  • Gwamna Peter Mbah ya rantsar da sababbin kwamishinoni shida tare da sauya wasu ma'aikatu don ƙarfafa aiki a jihar Enugu
  • Majalisar jihar Enugu ce ta fara tantance sababbin kwamishinonin da suka haɗa da na ayyuka, lafiya, makamashi da kasuwanci
  • Gwamna Mbah ya bukaci sababbin kwamishinonin da su fara aiki nan take, yana mai cewa gwamnati na da manyan burace-burace a gabanta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Enugu – A ranar Laraba, Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu ya sauya mukaman wasu kwamishinoni uku tare da rantsar da sababbin kwamishinoni shida da aka naɗa.

Gwamna Mbah ya kuma raba muƙamai ga sababbin kwamishinonin bayan da Chizoba Ogbodo, wakiliyar ma'aikatar shari'a, ta rantsar da su a gidan gwamnati da ke Enugu.

Gamnan Enugu, Peter Mbah ya yi sauye-sauye a majalisar zartarwarsa, ya rantsar da sababbin kwamishinoni
Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah yayin da yake jawabi a wani taron Ohanaeze Ndigbo a Janairun 2025. Hoto: @PNMbah
Source: Twitter

Hakazalika, Gwamna Mbah ya rantsar da Godwin Anigbo a matsayin shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Enugu, inji rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Cacar baki ta kaure tsakanin Akpabio da Barau da aka zo tantance wani tsohon sanata

An gudanar da bikin rantsar da kwamishinonin ne bayan majalisar jihar Enugu ta tantance kuma ta tabbatar da sunayen wadanda aka naɗa.

An rantsar da sababbin kwamishinoni 6

A makon jiya ne aka rahoto cewa Gwamna Mbah ya mika sunayen kwamishinonin da yake so ya nada zuwa gaban majalisar domin tantancewa.

Sabbin kwamishinonin da aka rantsar da ma'aikatar su:

  1. Benjamin Okoh - Ayyuka da abubuwan more rayuwa
  2. Benedett Okoli - Bunkasa jama'a da kawar da talauci
  3. Franklin Ogbonna - Harkokin makamashi da ma’adanai
  4. Samuel Ogbu-Nwobodo - Kasuwanci, zuba jari da masana’antu
  5. Ben Collins Ndu Jr. - Harkokin Ruwa
  6. George Ugwu - Lafiya

Garambawul a ma'aikatun jiha Enugu

George Ugwu ya maye gurbin Emmanuel Obi da ya riƙe kujerar kwamishinan lafiya tun daga shekarar 2015 a zamanin tsohon gwamna Ifeanyi Ugwuanyi.

An sauya ma Felix Nnamani mukami daga kwamishinan ma’aikatar ruwa zuwa ma’aikatar kwadago da ayyuka, inda zai maye gurbin Chika Ugwuoke wanda aka tsige daga kujerar makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Duniya kenan: Gwamna ya ji ba daɗi, hadiminsa kuma tsohon ɗan majalisa ya rasu

Haka nan, an dage Gerald Otiji daga ma’aikatar ayyuka zuwa ma’aikatar gidaje, yayin da Malachy Agbo ya koma ma’aikatar yada labarai daga ma’aikatar bunkasa jama'a da yaki da Talauci.

Malachy Agbo ya maye gurbin Aka Eze, wanda ya yi murabus domin tsayawa takarar shugabancin ƙaramar hukumar Udenu, kuma ya yi nasara.

Gwamnan Enugu ya bukaci sababbin kwamishinonin da ya nada da su fara aiki gadan gadan
Peter Mbah, gwamnan jihar Enugu yana jawabi wani taro da aka gudanar a gidan gwamnati. Hoto: @PNMbah
Source: Twitter

“A fara aiki cikin gaggawa” – Gwamna Mbah

A yayin rantsar da kwamishinonin, Gwamna Mbah ya jaddada cewa babu lokacin ɓatawa, kuma ya bukace su da su fara aiki nan take.

Ya ce cikin shekaru biyu da suka gabata, gwamnatinsa ta lasawa jama’ar jihar da ma Najeriya gaba ɗaya zuma a baki kan manyan ayyukanta, don haka ba za ta gaza a kowanne fanni ba.

A cewarsa:

“Ya zama wajibi a gare ku ku fara aiki ba tare da ɓata lokaci ba, babu lokacin shakatawa ko hutu.
“Mun tsara manyan buruka masu yawa, kuma kowace ma’aikata za ta taka muhimmiyar rawa wajen cimma waɗannan buruka.”

Uba Sani ya rantsar da sababbin kwamishinoni

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Uba Sani ya yi nadin sababbin kwamishinoni domin inganta shugabanci a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya yi zarra, Abba ya ƙara samun lambar gwarzon gwamnoni a Najeriya

Mai girma Gwamna Uba Sani ya nada Farfesa Abubakar Sambo a matsayin kwamishinan Ilimi, sannan aka sauyawa Farfesa Sani Bello ma’aikata.

Gwamnan ya ce yana sa ran sababbin kwamishinonin za su kawo sauyi a ma’aikatunsu tare da samar da hanyoyin magance matsalolin jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com