Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin Akpabio da Barau da Aka Zo Tantance Wani Tsohon Sanata

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin Akpabio da Barau da Aka Zo Tantance Wani Tsohon Sanata

  • Sanata Barau Jibrin ya bayyana rashin jin daɗinsa game da tantancewar Tijani Kaura duk da kasancewarsa tsohon dan majalisar dattawa
  • Sai dai, Sanata Godswill Akpabio ya yiwa Barau martani da cewa an bi ka'ida wajen tantance Kaura kuma ba zai bayar da hakuri ba
  • Daga bisani majalisar ta tabbatar da nadin Tijani Kaura matsayin mamban hukumar SSDC, duk da ce-ce-ku-cen da aka samu a baya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - An yi musayar yawu tsakanin shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da mataimakinsa, Barau Jibrin a ranar Laraba.

Shugabannin sun samu sabanin ne yayin tantance tsohon Sanata Tijani Yahaya Kaura a kokarin tabbatar da nadinsa a matsayin ɗan kwamitin hukumar raya yankin Kudu maso Kudu (SSDC).

An samu sabani tsakanin Sanata Barau Jibrin da Godswill Akpabio a ranar Laraba
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio da mataimakinsa, Sanata Barau Jibrin a zauren majalisar. Hoto: @barauijibrin
Source: Facebook

Sanata Kaura, ya wakilci Zamfara ta Arewa a majalisar kuma ya rike shugabancin kwamitin al'amuran tsarin wakilci a ma'aikatun tarayya, inji rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Fatima Alkali ta ki karbar mukamin da Tinubu ya ba ta, majalisa za ta tantance Farfesa Yusuf

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Barau ya soki tantance Kaura

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya naɗa Sanata Tijjani Kaura matsayin mamban SSDC domin ya wakilci yankin Arewa maso Yamma a hukumar.

A zaman majalisar na ranar Laraba, Sanata Barau Jibrin ya soki yadda aka bi ka’ida wajen tantance Kaura duk da cewa tsohon sanata ne.

Ya ce ya kamata majalisar ta tabbatar da nadin Kaura kai tsaye ba tare da an yi masa wasu tambayoyi ba kamar yadda ake yi wa sababbin mambobi.

A cewarsa:

“Wanda aka naɗa abokin aikina ne a wannan majalisa. Ban san dalilin da ya sa aka ce dole sai ya hau mumbarin tantancewa ba. Ya kamata kawai a amince da nadinsa.
"Ya taba shugabantar kwamitin tsarin wakilci a majalisa kuma ɗaya ne daga cikinmu. Saboda haka, bai kamata a ce sai an wani tsaya tantance shi ba. Shugaban majalisa, ya kamata mu guji irin haka nan gaba.”

Kara karanta wannan

Fulani makiyaya sun dimauce da aka kai musu hari da dare, an sace shanu

Daga bisani, majalisar ta tabbatar da nadin Kaura bayan kwamitin da ke kula da hukumar SSDC ya gabatar da rahoton da ya nuna cancantarsa.

Sanata Akpabio ya yiwa Barau martani

Da yake mayar da martani ga Barau, shugaban majalisar, Sanata Akpabio ya yaba da cancantar Kaura, amma ya dage cewa matakin da majalisar ta dauka na ci gaba da tantancewar yana kan tsari.

Akpabio ya yiwa Barau martani da cewa:

“Ba za mu ba da hakuri don bin ka'ida wajen tantance shi ba. Duk abin da za a yi, to ya kamata a yi shi ne bisa tsari.
“Ina taya tsohon sanata Kaura murna. Ina fatan zai kawo gagarumin ci gaba a hukumar SSDC.”

Duk da hakan, Sanata Barau ya nuna takaicinsa kan yadda za a ce a tsaya bin wasu matakan tantance tsohon Sanata alhalin ana iya daga masa kafa tare da amincewa da nadinsa.

Akpabio ya ce ba zai bayar da hakuri ba don an tantance tsohon sanata kan mukamin da aka nada shi
Zauren majalisar dattawan Najeriya da ke a babban birnin tarayya Abuja. Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Tsaikon tantance Sanata Tijani Kaura

Hukumar SSDC na ɗaya daga cikin sababbin hukumomin raya yanki da aka kafa domin shawo kan matsalolin zamantakewa, tattalin arziki da muhalli a yankin Kudu maso Kudu.

Kara karanta wannan

Majalisa ta mika bukata ga Tinubu, ta nemi a girmama marigayi Dantata

A ranar 26 ga Yuni, 2025, majalisar dattawa ta tabbatar da naɗin tsohon mataimakin shugaban majalisar wakilai, Chibudom Nwuche, a matsayin shugaban SSDC, inji rahoton Premium Times.

An kuma tabbatar da nadin Usoro Offiong Akpabio daga jihar Akwa Ibom a matsayin darakta janar na hukumar, tare da mambobi 13 na kwamitin gudanarwa da daraktoci masu zartarwa 5.

Sai dai an samu ce-ce-ku-ce a lokacin tabbatar da Kaura domin an cire sunansa daga jerin wadanda za a tantance bayan da ya kasa mika muhimman takardu kuma ya ƙi bayyana a gaban kwamitin tantancewa.

Kwamitin ya ce za a iya sake duba batunsa idan har ya yanke shawarar gabatar da takardunsa da kuma bayana gaban kwamitin tantancewa.

Majalisa ta karbi sunaye daga Tinubu

Tun da fari, mun ruwaito cewa, bayan kafa sababbin hukumomin raya yankuna uku, Shugaba Bola Tinubu ya aikawa majalisa sunayen shugabanni don tantancewa.

Tsohon Sanata Olubunmi Adetunbi, Cosmas Akiyir da Chibudom Nwuche su ne shugabanni da aka gabatar don jagorantar hukumomin.

Majalisar dattawa ta tura sunayen zuwa kwamitocin da suka dace domin tantancewa kafin amincewa da nadin a hukumance.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com