Sauki Ya Samu, NNPCL Ya Sake Rage Farashin Fetur Karo na 2 a cikin Mako
- Yayin da ake cigaba da kuka game da tsadar mai a Najeriya, kamfanin NNPCL ya sake rage farashin litar fetur
- Kamfanin ya rage farashin ne zuwa N890 a Abuja, bayan rage kuɗin zuwa N895 a makon da ya gabata
- A wasu wuraren Abuja kamar Kubwa da Wuse, an lura da sabon farashin, amma a Lagos farashin ya tsaya a N865
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ya sake rage farashin litar fetur a yayin da ake kuka kan tsadar man a Najeriya.
An tabbatar da cewa kamfanin NNPCL ya rage farashin litar fetur zuwa N890 a Abuja bayan ragewa a makon jiya.

Source: Getty Images
TheCable ta lura a ranar Laraba cewa an sauya farashin fetur a 'Federal Housing', Kubwa da Wuse, 'Zone 3' da ke birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan
Gaskiya ta fito: An ji dalilan da suka jawo naɗa Ministan Tinubu a matsayin shugaban APC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farashin fetur da NNPCL ya fitar a baya
Hakan na zuwa ne bayan kara kudin litar fetur a karshen watan Yunin 2025 da kamfanin ya yi da jawo ce-ce-ku-ce.
Kamfanin ya yi ƙari kan farashin da yake sayar da kowace lita a gidajen man da ke ƙarƙashinsa a wasu wurare.
A gidajen man NNPCL da ke Abuja da Lagos an lura da ƙarin da aka samu kan yadda ake siyar da kowace litar man fetur.
A babban birnin tarayya watau Abuja, farashin kowace litar man fetur ya koma N945 saɓanin N910 da ake sayarwa a baya.

Source: Facebook
Farashin fetur ya saba a Lagos da Abuja
Sabon farashin ya biyo bayan rage farashin da kamfanin ya yi makon da ya gabata zuwa N895, wanda ke nufin ragin N5.
Sai dai farashin litar fetur ya ci gaba da kasancewa N865 a Lagos a wasu wuraren a fadin Najeriya baki ɗaya.
A farkon watan Yuli, matatar Dangote ta saukar da farashin litar fetur daga matarta zuwa N820, mako guda bayan ta saukar da shi zuwa N840.
Farashin wasu gidajen mai a Abuja
Kamfanin MRS Oil, daya daga cikin abokan hulɗar Dangote, har yanzu yana sayar da fetur a N885 a Abuja, cewar rahoton Daily Post.
Domin magance damuwar da ake da ita kan farashin fetur da kalubalen wadatar fetur, gwamnatin tarayya ta tsara taron kasa a ranakun 23 da 24 ga Yulin 2025.
Francis Ogaree, daraktan kula da matatun mai da harkokin sufuri a hukumar NMDPRA, ya ce za a tattauna kan daidaiton farashi da wadatar danyen mai.
Dillalin fetur ya tattauna da Legit Hausa
Hussaini Muhammad ya ce a kullum dai ana samun rayuwar farashin duk da bai taka kara ya karya ba.
Ya ce:
"Abokan hulda da dama suna korafi cewa ragin N5 zuwa N10 ba shi ne mafita ba."
Hussaini ya ce sauƙin da ake bukata shi ne a ji an rage kamar daruruwa a nan ne hukumomi za su yabo.

Kara karanta wannan
Sojoji sun daƙile mugun shirin ƴan ta'adda, sun kashe mai ɗaukar bidiyo domin yaɗa ƙarya
Tankar mai ta kama da wuta a Oyo
Kun ji cewa wata tanka maƙare da fetur ta yi bindiga a yankin Celica da ke Ibadan, inda gobara mai ƙarfi ta tashi da misalin ƙarfe 6:30 na yamma.
Majiyoyi sun ce ma’aikatan kashe gobara daga jiha da tarayya sun shawo kan wutar cikin lokaci, inda suka hana ta bazuwa zuwa gidan man NNPC.
An tabbatar da cewa lalacewar birki ne ya haddasa hatsarin, inda tankar ta yi karo da wata mota ƙirar Prado, amma babu asarar rai sai motoci da suka ƙone.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
