Sheikh Sani Rijiyar Lemo Ya Yi wa Dangin Buhari Nasiha Mai Ratsa Zuciya a Daura
- Fitaccen malamin addini, Sani Rijiyar Lemo, ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayi Shugaba Muhammadu Buhari a Daura
- Farfesan musuluncin ya shawarci iyalan su ci gaba da yi wa marigayin addu'a, yana mai cewa hakan shi ne mafi alheri a gare shi
- Malamin ya ambato hadisin Manzon Allah SAW game da irin abin da mamaci ke ci gaba da amfana daga iyalan shi bayan mutuwa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Farfesa Muhammad Sani Umar Musa, Rijiyar Lemo, ya kai ziyara Daura domin yi wa iyalan shugaba Muhammadu Buhari ta'aziyya.
Ziyarar ta zo ne a wani bangare na girmamawa da nuna alhini bayan rasuwar tsohon shugaban kasar Najeriya, wanda ya rasu a birnin Landan yana da shekara 82.

Kara karanta wannan
'Ya yi mani albishir zan yi tazarce,' Tinubu ya fadi wanda ya taimaka ya zama shugaban kasa

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai game da nasihar da malamin ya yi a cikin wani bidiyo daga shafin Daga Malamanmu ya wallafa a Facebook.
Farfesa Rijiyar Lemo ya bayyana muhimmancin yin addu’a ga mamaci tare da jaddada cewa hakan shi ne mafi kyawun abu da ‘yan uwa da ‘ya’ya za su iya yi masa.
Nasihar Sani Rijiyar Lemu ga dangin Buhari
A yayin ta’aziyyar, malamin ya jaddada cewa addu’a ce mafi girma da mamaci ke ci gaba da amfana da ita bayan mutuwa.
Ya bayyana cewa idan da akwai wani abu mafi alheri fiye da addu’a, da Manzon Allah (SAW) ya ambace shi a cikin hadisin da ya yi magana kan abin da mamaci zai samu daga iyalan shi.
Hadisin da aka jawo wajen makokin Buhari
Malamin ya ambaci hadisin Manzon Allah (SAW) inda ya ce idan mutum ya rasu, ayyukansa suna yankewa sai guda uku – daga ciki akwai ɗa nagari wanda ke yi wa iyayensa addu’a.

Kara karanta wannan
An soki Rarara kan rashin ta'aziyya ga Buhari, ya wallafa bidiyon da ya tayar da ƙura
Ya ce wannan ya nuna cewa addu’a ita ce abin da ya fi dacewa da dacewa a yi wa mamaci, ba sadaka ko yanka ba, sai dai a roƙi Allah Ya gafarta masa.
A kan haka malamin ya bukaci dangin Buhari da suka hada da 'ya'yan shi da su dage da yi masa addu'a domin fatan Allah ya masa rahama.

Source: Facebook
Yadda ake zuwa ta'aziyya gidan Buhari
Tun bayan rasuwar Buhari, iyalansa a Daura na ci gaba da karɓar baki daga manyan mutane da shugabanni daga ciki da wajen Najeriya.
Ziyarar Farfesa Rijiyar Lemo na daga cikin jerin manyan baki da suka bayyana alhini da kuma yi wa marigayin addu'ar samun rahama.
A lokacin ta'aziyyar, Legit ta hango ɗan tsohon shugaban kasar, Yusuf Muhammadu Buhari na zaune kusa da Farfesa Sani Rijiyar Lemo.
Dangin Buhari sun yi wa jama'a godiya
A wani rahoton, kun ji cewa dangin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari sun yi wa jama'a godiya bayan gama zaman makoki.
Malam Mamman Daura ne ya yi magana a madadin dangin kuma ya yaba da rawar da shugaba Bola Tinubu ya taka bayan rasuwar Buhari.
A bayanin da ya yi, Mamman Daura ya ambaci sunayen wasu mutane da suka haura 30 da suka hada da 'yan siyasa da sarakuna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng