Bidiyo: Fusatattun Matasa Sun Tare Titin Kano zuwa Zaria, Sun Hana Motoci Wucewa
- Wasu fusatattun matasan Kano sun toshe hanyar Kano zuwa Zaria bayan ayarin motocin banki sun buge adaidaita sahu har ta kife
- Shaidu sun ce jami’an tsaron da ke rakiyar motocin bankin sun harba hayaki mai sa hawaye, lokacin da aka tunkare su kan hadarin
- DPO na Na'ibawa ne aka ce ya lallashi matasan, inda ya taimaka aka kwashe wadanda suka jikkata zuwa asibiti don ba su agaji
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - An samu cunkoson ababen hawa a hanyar Kano zuwa Zaria, musamman a yankin gadar sama ta Na’ibawa, a ranar Talata.
An rahoto cewa fusatattun 'yan adaidaita sahu sun toshe hanyar na sa’o'i domin nuna fushi kan raunin da wasu fasinjoji biyu suka samu sakamakon hadari da ayarin motocin banki dauke da kudade ya haddasa.

Kara karanta wannan
Gwamnonin 1999 sun nemi Tinubu ya ajiye raba tallafi, ya samar da ayyuka ga matasa

Source: Twitter
Matasa sun toshe titin Kano zuwa Zaria
Shaidun gani da ido sun fadawa jaridar Daily Trust cewa motocin banki da ake zargin suna dauke da kudi ne suka bangaje wani keke napep, ya fadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce ayarin motocin sun ki tsayawa su taimaki mutanen cikin adaidaita sahun suke duk da sun ga cewa sun yi mummunar faduwa a kusa da dagar saman Na'ibawa
Shaidu sun ce jami’an tsaron da ke rakiyar motocin bankin sun harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa jama’ar da suka taru domin ceto wadanda suka jikkata.
Wannan dalili ne ya sa aka ce masu Keke napep da aka fi sani da adaidaita sahu da kuma matasa da ke wajen suka nuna bacin ransu tare da toshe babban titin.
Shaida ya fadi abin da ya faru a Kano
Muhammad Sa’idu, daya daga cikin shaidun, ya ce sai da DPO na 'yan sanda na yankin ya shiga tsakani kafin matasan suka yanke shawarar janyewa daga kan hanyar.
Ya ce:
“Muna zaune a nan kusan karfe 9:00 na safe, sai muka ga gungun motocin banki masu dauke da kudi suna gudu, sai muka ga an bude kofar daya daga cikin motocin da ke rakiyarsu, ana girgiza sanda, ana gargadin mutane su kauce daga hanya.
“Da suka wuce kadan sai kofar motar ta bugi wani adaidaita sahu har ya kife kasa, har ma daya daga cikin jami’an tsaron ya kara bugun keken da sanda.
"Mutane sun je su nemi yin magana da su, sai suka harba hayaki mai sa hawaye don tarwatsa kowa, sannan suka ja motoci suka wuce suka bar wadanda suka jikkata cikin jini.”
DPO ya kwantar da tarzomar da ta tashi
Saboda yadda aka bar wadanda suka jikkata ba tare da taimako ba, matasan da suka hada da direbobin adaidaita sahu suka toshe titin, wanda shi ne hanyar zuwa Kaduna da Abuja daga Kano, inda suka kona tayoyi da burin neman adalci.

Source: Original
Wani shaidar, Auwal Ahmad, ya ce DPO ne ya iso wajen da kansa ya lallashi matasan tare da kai wadanda suka jikkata asibiti.
Ya kara da cewa:
“DPO ne ya taimaka aka dauke wadanda suka jikkata aka kai su asibiti, sannan ya yi alkawarin cewa za a kula da su sosai, wannan ne ya kwantar da hankalin jama'a.”
Ya kuma ce gungun motocin bankin na barin Kano ne kullum da safe zuwa Abuja, sannan su dawo da yamma.
A lokacin da manema labarai suka kai ziyara wajen da lamarin ya faru, an dawo da zaman lafiya.
Kalli bidiyon abin da ya faru wanda wani Alameen Muhammad Gama ya wallafa a shafinsa na Facebook:
Karin bayani kan rufe titin Na'ibawa
Legit Hausa ta tuntubi Buhari Ibrahim da ake yi wa lakabi da Likaku, wanda ke aiki a ofishin kungiyar NURTW a tashar mota ta kusa da gadar Na'ibawa don samun karin bayani.

Kara karanta wannan
MTN, Airtel, Glo da sauran kamfanonin sadarwa sun yi gargaɗi, za a iya ɗauke sabis a jihohi 16
Buhari Likaku ya ce mutane sun fusata da abin da ya faru sosai, saboda ana ganin kamar an buge keken ne da gangan, don kawai jami'an su nuna suna da karfin iko.
"Ni ina can ina raba tikitin shiga mota, sai muka ji kara alamar an yi banka. Muka tattaso domin ganin abin da yake faruwa, sai mu ka ga keke ta fadi.
"Motocin da suka zo wucewa, irin masu daukar kudi a banki din nan, da wasu motocin jami'an tsaro, sun ture keken, da mutane a ciki.
"Ban karasa wajen ba a lokacin, amma wadanda ke wajen sun kai dauki, sun tayar da keken, sun ciro mutanen ciki. Lokacin da ni na karasa, an watsa barkonon tsohuwa.
"Duk mun bar wajen muna rufe ido da toshe hanci. To a nan dai matasa suka nuna basu yarda ba, 'yan keke suka kashe hanya, aka rika kona taya, har dai DPO ya zo ya ba da hakuri."
An rasa rayuka kan titin Zaria-Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani hatsarin mota mai muni da ya afku a jihar Kano ya yi sanadin mutuwar mutane tara, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

Kara karanta wannan
Zamfara: An shiga tashin hankali bayan samun gawar malamin Musulunci a mugun yanayi
Kakakin hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Kano, Abdullahi Labaran, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne tsakanin wata babbar mota da adaidaita sahu.
Ya ce hatsarin da ya afku a hanyar Kano zuwa Zaria, wanda ya rutsa da mutum 12, ya jawo tsaikon ababen hawa yayin da ake kokarin kwashe mutanen.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

