Bayan Kwanaki 2 Yana Jinya, Likitoci Sun Fitar da Bayanan Lafiyar Gwamna Dikko Radda

Bayan Kwanaki 2 Yana Jinya, Likitoci Sun Fitar da Bayanan Lafiyar Gwamna Dikko Radda

  • Gwamnan Katsina, Dikko Ummaru Raɗɗa ya samu izinin komawa bakin aiki daga likitoci bayan hatsarin da ya rutsa da shi ranar Lahadi
  • Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa likitoci sun tabbatar da cewa gwamna ya warke sarai, kuma sun sallame shi daga asibiti
  • Tun farko Malam Dikko Raɗɗa ya gamu da ƙaramin hatsari a titin Daura zuwa Katsina yayin da ya fita yin wasu ayyukan al'umma

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - An sallami Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda daga asibitin da ya karɓi kulawar likitoci bayan da ya samu hatsarin mota a ranar Lahadin da ta gabata.

Legit Hausa ta kawo rahoton cewa Gwamna Radda ya gamu da hatsarin mota a kan hanyar Daura zuwa Katsina, titin da yake yawan zirga-zirga tun bayan rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

ADC: Atiku da El Rufai sun fara fuskantar abin da ba su yi tsammani ba daga manyan Arewa

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda.
An sallami gwmanan Katsina, Malam Dikko Radda daga asibiti Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed ya wallafa a shafinsa na Facebook jiya Talata, ya ce an sallami Dikko Raɗɗa daga asibiti.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Likitoci sun tabbatar da lafiyar Dikko Raɗɗa

Ya ce kwararren likitan Gwamnan ya tabbatar da cewa yana cikin ƙoshin lafiya kuma yana iya ci gaba da ayyukansa na ofis gaba ɗaya ba tare da wani jinkiri ba.

A sanarwar, Gwamna Radda ya yi godiya ta musamman ga dukkan ‘yan Jihar Katsina, abokai, abokan aiki, da kuma masu yi masa fatan alheri daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Gwamna Radda ya yi wa al'umma godiya

Gwamnan ya yiwa kowa godiya ta musamman bisa yadda suka yi addu’o’i da goyon baya a lokacin da yake kwance a asibiti na ɗan gajeren lokaci.

Sanarwar ta bayyana cewa Gwamna Radda zai ci gaba da aiwatar da ajandar canji ta “Gina makomarku” wadda ke nufin kawo cigaba da walwala ga Jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Bayan Rasuwar Buhari, Sheikh Pantami ya yi magana kan takarar da ake so ya nema a 2027

"Na yi matuƙar jin daɗin addu’o’i da goyon bayan da jama’ar mu suka nuna mani. Wannan ƙaunar da kuka nuna ta ƙara mani ƙwazo da jajircewa wajen ci gaba da yi wa Jihar Katsina hidima,” inji Gwamna Radda.

A ranar Lahadi da yamma ne Gwamnan ya samu ƙaramin hatsarin mota a hanyar Daura zuwa Katsina, a yayin da yake gudanar da ayyukan ofis don hidimar al’ummar Katsina.

Gwamna Dikko Radda.
An bai wa gwamna Dikko Radda damar komawa bakin aiki bayan hatsarin mota Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Ibrahim Kaula Mohammed ya tabbatar da cewa Gwamnan yana cikin ƙoshin lafiya kuma ba ya da wata mummunar rauni da ya samu.

Bayan kammala gwaje-gwaje da kulawa ta tsawon kwanaki biyu, likitoci sun tabbatar wa gwamnan cewa ya warke sarai, zai iya komawa bakin aiki.

Gwamna Raɗɗa ya lashe lambar yabo

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya lashe lambar yabo ta gwamnan da ya fi kowane aiki a shekarar 2025.

An karrama Gwamna Radda ne bisa namijin ƙoƙarin da yake yi wajen sauya Jihar Katsina ta fuskar inganta ababen more rayuwa, ilimi, lafiya, tsaro da ƙarfafa tattalin arziki.

A wani biki mai ƙayatarwa da aka shirya domin ba da lambar yabon, Gwamna Raɗɗa wanda ya samu wakilcin kwamishinar mata, ya sadautar da kyautar ga al'ummar jihar Katsina.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262