Za a Samar wa Matasa Miliyan 1 Ayyuka Ta Hanyar Noma a Jihohi 22

Za a Samar wa Matasa Miliyan 1 Ayyuka Ta Hanyar Noma a Jihohi 22

  • Gwamna Hyacinth Alia ya ce jihar Benue za ta taimaka wa Najeriya ta zama jagaba a fitar da waken suya zuwa kasashen duniya
  • Sabon shirin ƙara samar da waken suya zai samar da aikin yi miliyan 1 tare da Naira tiriliyan 3.9 na kudin shiga
  • An gabatar da shirin ne a wani taron na musamman da aka yi a Abuja, kuma manyan jami'an gwamnati da kamfanoni sun halarta

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin jihar Benue ta bayyana cewa Najeriya na kan hanyarta ta zama ƙasa mafi samar da waken suya a duniya.

Hakan na zuwa ne yayin da shirin farfado da noman waken suya tare da habaka tattalin arzikinta da samar da miliyoyin ayyukan yi ga matasa da manoma.

Kara karanta wannan

ICRC ta gano babbar matsalar da ta tunkaro Arewa sakamakon ta'addanci

Jami'an gwamnati bayan kammala taron shirin noman waken suya a Abuja
Jami'an gwamnati bayan kammala taron shirin noman waken suya a Abuja. Hoto: @benuestategovt
Source: Twitter

Gwamnatin Benue ta wallafa a X cewa gwamnan Hyacinth Iormem Alia ne ya bayyana haka a ranar Talata, 22 ga Yuli, 2025, a wajen ƙaddamar da shirin faɗaɗa noman waken suya a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a samar da ayyuka miliyan 1 ta noma

A cewar Gwamna Alia, Benue za ta taimakawa sabon tsarin noman waken suya da aka tsara don samar da N3.9tn a kowace shekara da kuma ayyukan yi har miliyan 1 a jihohi 22 da Abuja.

Alia ya bayyana cewa jihar Benue na da kusan rabin gonakin da ake noma waken suya a Najeriya, tana kuma samar da kaso mai tsoka daga cikin tan 758,000 da ake samu a ƙasa baki ɗaya.

Ya ƙara da cewa gwamnatin Benue, ta hanyar Kamfanin Bunƙasa Noma na Jihar, tana gudanar da horo da bai wa manoma kayan aiki a kananan hukumomi 15 da ke samar da waken suya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi bayani yayin da aka fara taron daidaita farashin fetur a Abuja

Za a kara yawan noma waken suya

A cewar Alia, jihar na shirin ƙara yawan waken suya daga tan 202,000 zuwa tan 400,000 a cikin shekaru uku, lamarin da zai kawo gagarumin cigaba ga tattalin arzikin jihar da ƙasar baki ɗaya.

Ya ce hakan zai taimaka wajen cimma burin samar da Naira tiriliyan 3.9 na kudin shiga da kuma taimaka wa dubban iyalai da matasa su samu ayyukan yi da hanyoyin dogaro da kai.

Gwamna Alia ya bukaci hadin gwiwar gwamnatin tarayya, kamfanoni, da kungiyoyi wajen tabbatar da cewa waken suya ya zama amfanin gona mai matuƙar alfanu ga Najeriya.

Minista ya yaba da ƙoƙarin Gwamna Alia

Ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana muhimmancin waken suya ga tattalin arzikin Najeriya da lafiyar al’umma.

Ya yi kira ga dukkan kwamishinonin noma na jihohi su rungumi shirin noma waken suya cikin hangen nesa da haɗin kai da manoma da masu zuba jari da masana’antu.

Kara karanta wannan

'Juyin juya hali,' An kawo hanyar warware matsalolin Najeriya gaba daya

Gwamnan jihar Benue yana jawabi a gidan gwamnati
Gwamnan jihar Benue yana jawabi a gidan gwamnati. Hoto: @benuestategovt
Source: Twitter

Ministan ya yaba da ƙoƙarin Gwamna Alia na jagorantar jihar Benue da nasarorin da aka fara samu tun kafin aiwatar da sabon tsarin ya kammala.

Taki ya fara hana noma a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa tsadar takin zamani ya fara kawo matsala ga manoman Najeriya a daminar bana.

Wasu manoma sun bayyana cewa sun daina shuka abubuwan da suke bukatar takin zamani saboda kaucewa tafka hasara.

A zantawar da Legit ta yi da wani manomi a Gombe, ya bayyana cewa ba lallai su kai labari ba idan har ba a samu saukin kudin taki ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng