Zargin Rashawa: An ba Gwamna Wa'adin Awa 48, Ana So Ya Kori Sakatariyar Gwamnati

Zargin Rashawa: An ba Gwamna Wa'adin Awa 48, Ana So Ya Kori Sakatariyar Gwamnati

  • Kungiyar 'yan Ebonyi mazauna kasashen waje ta bukaci Gwamna Francis Nwifuru ya kori sakatariyar gwamnati, Grace Umezuruike
  • Shugaban ƙungiyar AEISCID ya caccaki gwamnatin Ebonyi kan yin shiru game da zargin sata da ake yi wa sakatariyar gwamnatin
  • Kungiyar ta bukaci EFCC ta fadada bincikenta kan mulkin Nwifuru da na tsohon gwamna Dave Umahi, don bankado rashawar da aka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ebonyi - Kungiya da ke wakiltar 'yan asalin Ebonyi da ke ƙasashen waje ta bukaci Gwamna Francis Nwifuru da ya kori sakatariyar gwamnatin jiha (SSG), Farfesa Grace Umezuruike.

A cikin wata sanarwa da ta aikawa Legit.ng a ranar Talata, 22 ga Yuli, ƙungiyar ta ce ta yi wannan kira ne bayan wani umarnin kotu na wucin gadi.

An bukaci gwamnan Ebonyi ya sallami sakatariyar gwamnatin jihar da ake zarginta da rashawa
Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru | Sakatariyar gwamnatin Ebonyi, Grace Umezuruike. Hoto: @FrancisNwifuru
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa a ranar 8 ga Yuli 2025 ne babbar kotun tarayya da ke Uyo ta bukaci a kwace sama da N1bn daga hannun sakatariyar da ake zargin kuɗin sata ne.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Rikakken dillalin kwayoyi ya shiga hannu bayan shekara 6 ana nemansa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babbar kotun ta baiwa hukumar EFCC damar ƙulle asusun banki da ke da alaƙa da Farfesa Umezuruike da mai taimaka mata, Ngene Nwanna Onyeabor.

Ƙungiyar ta caccaki gwamnatin Ebonyi

A cikin sanarwar, shugaban ƙungiyar AEISCID, Ambasada Pascal Oluchukwu, ya caccaki gwamnatin Ebonyi bisa yin shiru game da wannan lamari, inda ya bayyana hakan a matsayin abin kunya da kuma cin amanar jama’a.

“Halin ko in kula da gwamnati ke nunawa a kan wannan zargi mai girma, wanda ke da illa babba ga jihar da al’ummarta, abin takaici ne ƙwarai,” in ji Oluchukwu.

Ya ci gaba da cewa:

“Muna bukatar Gwamna Nwifuru ya sauke sakatariyar gwamnatin daga mukaminta cikin sa’o’i 48 domin a gudanar da bincike ba tare da katsalandan ba.”

Ya kuma ce karkatar da irin wannan kuɗi abu ne mai muni musamman ga jiha “inda ake ganin talauci yana yawo a fili.”

Kara karanta wannan

"An yi abin kunya," ADC ta tona abin da gwamnatin Tinubu ta yi a rasuwar Buhari

Ƙungiyar ta nemi a fadada binciken EFCC

AEISCID ta kuma bukaci EFCC da ta fadada binciken ta har zuwa wasu laifuffukan cin hanci da rashawa da ake zargi a mulkin yanzu da kuma na shekaru takwas na tsohon Gwamna Dave Umahi.

Jaridar Punch ta rahoto kungiyar ta kara da cewa:

“Zargin sata ya hana ayyukan ci gaba gudana kuma ya kara tsananta halin kuncin tattalin arziki da mutanen Ebonyi ke ciki.
“Ba wai kawai mulkin Nwifuru ba, magana ce ta a ceci jihar Ebonyi daga cin hanci da rashawa da ya zama ruwan dare.”

Ƙungiyar ta zargi tsohon gwamna Dave Umahi da ci gaba da yin tasiri a harkokin jihar, inda ta ce “Ebonyi ba ta iya numfashi da kyau saboda ya yi kane-kane a shugabancinta."

An bukaci EFCC ta gudanar da bincike kan gwamnatin Francis Nwifuru da tsohuwar gwamnatin Dave Umahi
Ana so EFCC ta binciki gwamnatin Francis Nwifuru kan zarge-zargen rashawa. Hoto: @FrancisNwifuru
Source: Twitter

Dalilin da yasa ya kamata a kori Umezuruike

AEISCID ta jaddada cewa bukatar da ta aike na a sauke Umezuruike daga mukami ya dace da ƙa’idojin mulki na gaskiya, wanda ake yi a duniya.

Kara karanta wannan

Gwamna, iyalan Sarki sun shiga matsala bayan birne basarake bisa tsarin Musulunci

“Da zarar an tabbatar da hujja kuma kotu ta kwace kuɗi daga asusun mutum, abu mafi dacewa shi ne wanda ake zargin ya bar ofis don gudun katsalandan a binciken,” inji ƙungiyar.

Ƙungiyar ta kuma shawarci gwamnatin Ebonyi da ta aike da bukatar shiga cikin shari’ar ta yadda idan aka ayyana kuɗin a matsayin mallakar gwamnati, za a iya dawo da su.

Grace Umezuruike ta zama sakatariyar Ebonyi

Tun da fari, mun ruwaito cewa, gwamnan Benue, Hyacinth Alia, ya naɗa Barista Aber Deborah a matsayin sabuwar sakatariyar gwamnatin jiha (SSG).

Nadin ya biyo bayan murabus da tsohon SSG, Farfesa Joseph Alakali, ya yi daga mukaminsa bisa dalilai na kashin kansa da bai bayyana ba.

Gwamna Alia ya amince da murabus ɗin Alakali, sannan a ranar Talata, 10 ga watan Satumba, ya naɗa Barista Deborah a matsayin wadda za ta gaje shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com