'Yan Sanda Sun Cafke Mutane 567, An Kwato Bindigogi, Motoci, Kayan Tsafi a Adamawa

'Yan Sanda Sun Cafke Mutane 567, An Kwato Bindigogi, Motoci, Kayan Tsafi a Adamawa

  • Rundunar ‘yan sandan Adamawa ta kama mutum 567 da ake zargi da laifuffuka iri-iri ciki har da garkuwa da mutane, fyade da safarar yara
  • CP Moris Dankwambo ya ce sahihan bayanan sirri ne suka taimaka wajen ceto yara 13 da aka safararsu daga Adamawa zuwa Anambra
  • Jami’ai sun kwato bindigogi, motoci, babura, kayayyakin tsafi da wayoyi, yayin da aka kama mata biyu da ake zargi da jagorantar safarar yara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Adamawa - Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama mutane 567 da ake zargi da aikata laifuffuka daban-daban tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

Rundunar 'yan sandan ta sanar da cewa ta ceto mutane hudu ne da aka sace su, sannan kuma ta kubutar da kananan yara 13 da aka yi safararsu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun nuna tsaurin ido, sun sace mutane 26 a mahaifar gwamnan Bauchi

Rundunar 'yan sandan Adamawa ta cafke masu aikata laifuffuka har mutum 567
Jami'an 'yan sanda sun kara kaimi wajen sintiri tare da kama masu laifi a Adamawa. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

'Yan sanda sun cafke masu laifi 567

Kwamishinan ‘yan sanda, Morris Dankwambo, ya bayyana hakan yayin da yake magana da manema labarai a ranar Litinin a hedkwatar rundunar da ke Yola, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

CP Morris Dankwambo ya bayyana cewa jami'an rundunar sun gudanar da samame a wurare daban-daban cikin jihar da wajenta.

“A kokarin hadin gwiwar jami’an yaki da garkuwa da mutane, sashen fikira, sashen dakarun kai farmaki, shugabannin ofisoshin 'yan sanda, rundunar ta kama mutane 567.
"Ana zargin wadanda aka kama aikata laifuffuka daban-daban ciki har da garkuwa da mutane, kisan kai, fashi da makami, safarar yara, fyade, cin zarafi na jima’i da sauransu."

- CP Morris Dankwambo.

An ceto yara 13 da aka yi safararsu

CP Dankwambo ya kara da cewa nasarar samamen ta samo asali ne daga sahihin bayanan sirri, wanda daga bisani ya kai ga babban aikin da ACP Shuaibu Wara ya jagoranta, inda aka kama wasu mata da suka “kware wajen satar yara da safararsu."

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Mamakon ruwan sama ya jawo ambaliya a gari, mutane 54 sun mutu

“A kwanan nan, an ceto yara 13 da aka yi safarar su daga Adamawa aka siyar da su ga wasu mutane a jihar Anambra,” in ji Dankwambo.

Kwamishinan ya bayyana cewa bincike na ci gaba da gudana kuma za a mika yaran ga iyayensu na gaskiya nan ba da jimawa ba.

Rundunar 'yan sanda ta ce ta kubutar da kananan yara 13 da aka yi safararsu a Adamawa
Taswirar Najeriya da ke nuna jihar Adamawa da ke a Arewa maso Gabashin kasar. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An kwato bindigogi, da kayan sata

Ya bayyana abubuwan da aka kama daga hannun wadanda aka kama da suka hada da:

“Bindigogin AK-47 guda shida, bindigogin harba ka labe guda uku, bindigu kirar hannu guda 11 da alburusai iri-iri.”

Sauran abubuwan da aka gano sun hada da motoci uku, kekunan Napep biyar, babura hudu da tankar gas guda biyu da aka sace.

Har ila yau, ya ce an gano kwamfutoci, wayoyin salula, kayan tsafi da wasu abubuwa daban-daban, a cewar rahoton The Nation.

Manyan wadanda ake zargi da aikata laifin da aka kama sun hada da:

“Mrs. Ngozi Abdulwahab, mazauniyar Jambutu a karamar hukumar Yola ta Arewa da Mrs. Uche Okoye, mazauniyar Kabiku a Nnewi, jihar Anambra.”

An bayyana wadannan mata biyu a matsayin “wadanda suka daɗe suna safarar yara daga jihar Adamawa zuwa jihar Anambra da sauran sassan ƙasar.”

Kara karanta wannan

Jagoran yan ta'adda ya shiga hannu, ya fara ambato abokan hulɗarsa bayan ya ji matsa

'Yan sanda sun kama 'Yan Shila a Adamawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan sandan Adamawa sun kama 'yan daba da aka fi sani da 'yan shila da suka addabi sassa daban-daban na jihar.

Suleiman Nguroje, kakakin rundunar ne ya tabbatarwa manema labarai da kamen, inda ya ce cikin yan shilar da aka kama akwai mata biyu.

Rundunar 'yan sandan ya nemi hadin kan al'umma ta hanyar ba su bayanan sirri na shawagin duk wasu da ba su aminta da su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com