Ana Zargin Gwamnan APC da Rashin Aiwatar da Umarnin da Tinubu Ya ba Shi
- Tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya ce babu wani mataki da aka dauka kan umarnin da Bola Tinubu ya bayar
- Ortom ya ce har yanzu gwamna Hyacinth Alia bai kira taron da Shugaban kasa ya umurta da a yi ba a jihar kan kashe al'umma
- Ya yaba da yadda Shugaba Tinubu ya kai ziyara bayan kisan Yelewata, yana mai cewa gwamnatin baya ba ta yi haka ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Benue - Tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana damuwarsa kan yadda har yanzu ba a dauki matakin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar ba.
Ortom ya ce Bola Tinubu ya bukaci a hada kai da manyan masu ruwa da tsaki domin shawo kan matsalar tsaro a jihar.

Source: Facebook
A yayin hira da tashar Channels TV, Ortom ya ce tun bayan umarnin Shugaban kasa da aka bayar a ranar 18 ga Yuni, babu wani zama da aka kira tsakanin gwamnati da sauran shugabanni a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Umarnin da Tinubu ya bayar a Benue
Shugaba Tinubu ya ziyarci jihar Benue ne bayan harin Yelewata da ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutum 100, inda ya bukaci a hada karfi da karfe wajen shawo kan rikicin.
Tsohon gwamna Ortom ya bayyana cewa ba a tuntube su ba ko kira wani taro tun bayan ziyarar Shugaban kasa.
Daily Trust ta wallafa cewa ya ce:
“Ba mu yi wani zama ba tun bayan ziyarar Shugaban kasa. Wata kila muna jiran gwamna ya kira mu domin mu je. Benue tamu ce, kuma ba za mu yarda hakan na faruwa ba.”
Ya kara da cewa harin Yelewata ya taba shi kai tsaye domin yankin na cikin karamar hukumar sa, kuma kakar shi daga can ta fito.
“Wannan gari gida ne a wurina,”
- Inji Ortom.
Ya tuna da yadda ya yi kokari a mulkinsa
Ortom ya bayyana irin matakan da ya dauka a lokacin mulkinsa domin dakile hare-haren makiyaya da kuma kare rayukan al’umma.
Ya ce ya hada kai da sarakunan gargajiya da hukumomin tsaro da kuma al’ummomi domin dakile rikice-rikicen.
Ortom ya yaba wa shugaba Tinubu
Ortom ya yaba da yadda Shugaba Tinubu ya dauki mataki bayan harin Yelewata, yana mai cewa gwamnatin da ta gabata ba ta taba daukar irin wannan mataki ba.
“A lokacin da aka kai harin Yelewata, shugaban kasa da kansa ya zo.
"Ya umurci jami’an tsaro da su kamo wadanda suka aikata laifin. Wannan bai taba faruwa a zamanin gwamnatin baya ba,”
Inji Ortom.

Source: UGC
Ortom ya yi magana kan zaben 2023
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya ce bai yi nadamar kin marawa Atiku Abubakar baya ba a 2023.
Samuel Ortom ya hada kai da wasu gwamnonin PDP da suka hada da Nyesom Wike na Rivers wajen juya wa Atiku baya.
Legit Hausa ta rahoto cewa Samuel Ortom ya bayyana cewa matakin da suka dauka shi ne ya fi dacewa a daidai lokacin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


