Manoma na cikin Tashin Hankali, Ambaliyar Ruwa Ta Yi Barna a Garuruwa 7 na Kebbi
- Ambaliyar ruwa a Kebbi ta lalata gonakin shinkafa a Yauri, Shanga da Ngaski, inda hakan ya jefa dubban manoma cikin damuwa
- Ahmed Sarkin Yaki ya tabbatar da aukuwar ambaliya a garuruwan Kwanji, Gebbe, Nasara, Ishe, Tungan Hakimi Mamuda, Buro da Kurdoso
- Kebbi da wasu jihohin da ke makwabtaka da ita kamar Neja, Sokoto da Kwara sun fuskanci ambaliyar ruwa mai muni a 2024 da 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kebbi - Ambaliyar da ta auku a Kebbi sakamakon cika da tumbatsar koguna ta lalata gonakin shinkafa a ƙananan hukumomin Yauri, Shanga da Ngaski na jihar.
An ce ambaliyar ta lalata gonakin shinkafa da dama a ƙananan hukumomin uku da ke ƙarƙashin masarautar Yauri, wanda ya jefa manoma cikin tashin hankali.

Source: Getty Images
Ambaliya ta yi barna a jihar Kebbi
Wani ɗan asalin yankin, Ahmed Sarkin Yaki ne ya tabbatar da aukuwar wannan iftila’in a Birnin Kebbi, yayin da yake zantawa da jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, garuruwan da ambaliyar ta yi wa manoma barna sun haɗa da Kwanji, Gebbe, Nasara, Ishe, Tungan Hakimi Mamuda, Buro da Kurdoso.
“Muna zargin ruwan kogunan Dolekaina, Jega da Tondi Gada ne ya balle, ya jawo ambaliiya a garuruwan.
“Muna roƙon shugabannin ƙananan hukumomin Yauri, Shanga da Ngaski da su kawo ɗauki ga manoman da ambaliya ta shafa."
- Ahmed Sarkin Yaki.
Kalubalen ambaliya a jihar Kebbi
Jihar Kebbi na fuskantar mummunar ambaliya a ‘yan shekarun nan, lamarin da ke da tasiri sosai ga fannin noma, musamman shinkafa, wadda jihar ke kan gaba wajen nomawa a ƙasar.
A shekarar 2024, ambaliya ta shafi ƙananan hukumomi 16 daga cikin 21 na jihar Kebbi, ciki har da Yauri, Shanga da Ngaski, inda ta lalata hekta 858,000 na gonaki, da amfanin gona kamar su shinkafa, masara da dawa.
Iftila’in ya yi sanadin mutuwar mutane 29, tare da raba dubban mutane da muhallansu, lamarin da ya haifar da fargabar ƙarancin abinci, inji rahoton Channels TV.
Ambaliya a jihohin da ke makwabtaka da Kebbi
Jihar Neja:
A watan Afrilu 2025, an samu ambaliya sakamakon ballewar ruwa daga dam ɗin Jebba, wanda ya shafi manoman rani fiye da 5,000, tare da lalata hekta 10,000 na gonakin shinkafa a karamar hukumar Mokwa kaɗai.

Source: Getty Images
Hakan ya shafi manoma a jihohin Kebbi, Sokoto, Katsina da Kano, inda aka yi asarar biliyoyin Naira tare da raba mutane fiye da 6,400 da muhallansu.
A wata ambaliyar da ta sake faruwa a Mokwa a watan Mayun 2025, an ce sama da mutane 150 suka mutu, yayin wa sama da mutane 3,500 suka rasa muhallansu, inji rahoton Aljazeera.
Jihohin Sokoto da Kwara:
Ambaliya ta 2024 da ke da nasaba da ruwa daga dam ɗin Goronyo da Kogin Rima ta haddasa asarar amfanin gona a Sokoto.
Ambaliyar ruwa a watan Afrilu 2025 daga dam ɗin Jebba ta shafi jihar Kwara sosai, inda aka yi asarar gonakin shinkafa da dama.

Kara karanta wannan
Kogi: Malamin jami'a ya mutu yana tsakiyar lalata da ɗalibarsa, an ga gawarsa a otal
Ambaliya ta yi barna a jihohi 2
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ambaliyar ruwa ta lalata gonakin al’umma a sassa daban-daban na jihohin Kebbi da Neja da ke Arewacin kasar nan.
Hukumar N-HYPPADEC ta bayyana tausayinta ga waɗanda iftila’in ya shafa tare da jinjina wa gwamnatin tarayya bisa ware Naira biliyan 3 domin rage radadin lamarin.
Kusan kowace shekara Najeriya na fuskantar ambaliya a jihohi da dama, musamman waɗanda koguna da ruwa ke gudana a cikinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

