'Yan Bindiga Sun Nuna Tsaurin Ido, Sun Sace Mutane 26 a Mahaifar Gwamnan Bauchi
- 'Yan bindiga sun kai hari mahaifiyar gwamnan Bauchi, watau Alkaleri, inda kashe mutum ɗaya tare da yin garkuwa da mutane 26
- Wani mazaunin Gale ya ce 'yan bindigar sun bude wuta kan mai uwa da wabi, kuma sun kashe mutum daya bayan sace mutanen
- Iyalan wadanda aka sace sun biya N1.5m domin kuɓutar da ɗaya daga cikin su, yayin da ragowar mutanen ke hannun miyagun
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bauchi – 'Yan bindiga sun sace mutane 26, sun kashe mutum ɗaya a hare-haren da suka kai ƙaramar hukumar Alkaleri, jihar Bauchi inda nan ne mahaifar Gwamna Bala Mohammed.
Wani mazaunin yankin, Burham S. Gale, ya ce 'yan bindigar sun bude wuta kan mai uwa da wabi a harin da suka kai daren Asabar a kauyen Gale da ke cikin gundumar Gwana.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Saurayi ya sari tsohuwar budurwarsa da adda, ya kashe mahaifiyarta

Source: Twitter
'Yan bindiga sun sace mutum 26 a Bauchi
Burham, wanda mahaifinsa na cikin waɗanda aka yi garkuwa da su a wani harin da ya gabata, ya shaidawa jaridar WikkiTimes cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mun fi kusa da gandun dabbobi na Yankari, don haka 'yan bindigar na yawan yawo a nan. Ana yawan cin karo da su a gona ko daji, amma ba sa cutar da kowa.
"A ranar, ina cikin wani shago ne lokacin da muka ji harbe-harbe. Kowa ya watse. Suka kama waɗanda ba su samu damar guduwa ba. Suka kwashe kayan shaguna, abinci da waya, sannan suka tafi da maza shida."
Ya ƙara da cewa daga baya 'yan bindigar sun saki mutane biyu daga cikin waɗanda suka sace; Mahaifinsa mai fama da rashin lafiya da wani mutum da ke da tabin hankali, inda suka yar da su a cikin daji kusa da kauyen.
A halin yanzu mahaifinsa yana karɓar magani a asibiti, yayin da sauran mutum huɗu ke ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwar.
Alkaleri: An tsinci gawar wata da aka sace
Burham ya ce wata mata da ta nemi tserewa cikin daji lokacin harin ta ji raunin harbin bindiga kuma an tsince ta tana zubar da jini a safiyar ranar Lahadi.
"Abin takaici, an tsince ta da raunin harsashi kuma ta rasu a hanya yayin da ake kokarin kai ta asibitin Gombe," inji Burham S. Gale.
Mazauna yankin sun koka da yadda jami’an tsaro ba su kawo dauki ba, duk da cewa akwai ofisoshin 'yan sanda da na sojoji a ƙauyukan Mansir da Digare da ke kimanin kilomita 10 kacal daga inda hare-haren suka faru.

Source: Original
An fara biyan 'yan bindiga N1.5m
Hamza Dogon Ruwa, wanda ƙaninsa na cikin mutum 20 da aka sace a harin ranar 4 ga Yuli 2025, ya bayyana cewa daga baya an saki mutum 11, yayin da sauran tara suke hannun miyagun.
A cewarsa, masu garkuwar sun kira su ta wayar mahaifiyarsu, inda suka cimma yarjejeniya kuma suka biya Naira miliyan 1.5 don kuɓutar da ɗan uwansu.
Hamza ya ce ƙungiyar sa-kai ta ƙauyen ta yi ƙoƙarin ceto mutanen amma ba ta yi nasara ba, sannan danginsu sun kai ƙorafi ofishin DSS da ke hedikwatar Alkaleri.
Ƙarin bayani kan harin garin Gale
Wani mazaunin ƙaramar hukumar Alƙaleri, Fantyz Guy, ya tabbatar da wannan labari ga Legit Hausa a ranar 22 ga Yulin 2025. Fantyz Guy ya ce:
"Tun shekaran jiya ne abin ya faru, da misalin karfe 8:00 na dare. A dalilin haka, akwai wata mata guda daya da ta rasa ranta.
"Mutuwar da ta yi ba wai an harbe ta da bindiga ba ne. Lokacin da ƴan bindiga suka shiga garin, to garin gudun ceton rai matar ta faɗi ta karye.
"Karyewar da ta yi tun bayan karfe 8:00 na dare, ba a samu damar kai ta asibiti ba sai washegari da safe. Ana kai ta Gombe saboda garin ya fi kusa da Gombe.
"Shigar su, sun yi harbe-harbe, sun kwashi kayan abinci, sai suka dauki matasa hudu suka dora masu kayan suka tafi da su cikin daji."
Gwamnan Bauchi ya kai dauki mahaifarsa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya tabbatar da mutuwar fiye da ‘yan bindiga 60 a wani artabu da ya faru a ƙaramar hukumar Alkaleri.
Ya ce mutane 21 ne suka rasa rayukansu a rikicin, ciki har da 'yan banga 13 da fararen hula takwas, inda ya yaba da jajircewar jami’an tsaro da matasan ƙauyen.
Gwamnan ya sanar da bayar da tallafi sama da Naira miliyan 70 ga iyalan waɗanda abin ya shafa tare da shirin ɗaukar sababbin ‘yan banga fiye da 2,100 a faɗin jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


