Ana Rade Radin Zai Shiga Jam'iyyar APC, An Hango Kwankwaso a Fadar Shugaban Kasa

Ana Rade Radin Zai Shiga Jam'iyyar APC, An Hango Kwankwaso a Fadar Shugaban Kasa

  • An hango jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Litinin
  • An rahoto cewa Sanata Kwankwaso ya halarci taron tattalin arzikin daji na kasa wanda kwamitin shugaban kasa na PreCEFI ya shirya
  • Taron ya mai da hankali kan yadda za a fitar da dala biliyan 2 daga tattalin arzikin daji tare da samar da ayyuka da ci gaba mai ɗorewa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – An hango ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a fadar shugaban kasa da ke Abuja, a ranar Litinin.

Kwankwaso ya halarci taron tattalin arzikin daji na Najeriya na 2025, wanda kwamitin shugaban kasa kan haɗa kan tattalin arziƙi da kuɗi (PreCEFI) ya shirya.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya isa fadar shugaban kasa taron da ake sa ran Tinubu zai halarta

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya halarci taron da kwamitin shugaban kasa ya shirya a Aso Rock
An gano Sanata Rabiu Kwankwaso da wasu shugabanni a taron tattalin daji a fadar shugaban kasa. Hoto: @SaifullahiHon
Source: Twitter

Shettima ya fadi illar lalacewar dazuka

Kwankwaso bai gabatar da jawabi a wajen taron ba, kuma bai yi magana da manema labarai ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Da yake jawabi a wajen taron, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya yi gargaɗi game da mummunan yanayin dazukan Najeriya da illolinsa ga tattalin arziki.

Shettima, wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban ma'aikatan shugaban ƙasa, Ibrahim Hadejia, ya ce dole a dauki matakan gaggawa don shawo kan matsalolin.

Wannan ya zo ne yayin da wanda ya kafa Netzence, Dokta Sadiq Sani, ya tabbatar da cewa kamfaninsa yana amfani da fasaha don buɗe damarmakin da suka kai sama da $2b a fannin daji.

Bayani kan kasashe masu cin moriyar dazuka

Da yake jawabi yayin buɗe taron, Shettima ya ce:

"Fiye da kashi 90 na dazukan Najeriya sun lalace, kuma ana rasa fiye da hekta 400,000 duk shekara, kuma halin da ake ciki ba wai rikicin muhalli ba ne."

Kara karanta wannan

Taron APC: Tinubu ya shiga tsaka mai wuya game da zakulo magajin Ganduje

Ya jaddada cewa ƙasar tana kan wani mahimmin lokaci kuma rashin kulawa da albarkatun daji kai tsaye yana talauta al'umma da mutanenta.

"Ba za mu iya raina muhimmancin dazukanmu ba. Su taska ce ta bambancin halittu, katako, tsirran magani, da sauran kayayyaki masu daraja waɗanda ke tallafa wa noma, kasuwanci, lafiya, da juriya ga sauyin yanayi, da kuɗi.
"Ku duba Vietnam, tana samun fiye da dala biliyan 15 duk shekara daga fitar da kayayyakin daji. Amazon na Brazil yana ba da gudummawar kashi 15 na GDP ɗin su daga dazuka kaɗai.
"Habasha ta samar da ayyukan yi 350,000 ta hanyar dashen bishiyoyi. Bai kamata Najeriya ta zuba ido ba, ya kamata ta jagoranci masana'antar daji ta Afirka."

- Kashim Shettima.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya halarcin taron tattalin arzikin daji a fadar shugaban kasa Abuja
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da mahalarta taron tattalin arzikin daji a fadar shugaban kasa. Hoto: @SaifullahiHon
Source: Twitter

Ziyarar Kwankwaso fadar shugaban kasa

Mai taimaka wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kan harkokin yaɗa labarai, Hon. Saifullahi Hassan, ya sanar a shafinsa na X cewa:

"Jagoran ƙasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya halarci taron farko na Nigeria tattalin arzikin daji da aka gudanar a yau Litinin, 21 ga Yuli, 2025, a dakin Banquet na fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

2027: Jigon NNPP ya ba Kwankwaso shawara kan takara da Tinubu

"An girmama shi a matsayin baƙo na musamman, kuma halartar sa ta ƙara armashi ga wannan taro na manyan jami’ai.
"Taron ya mayar da hankali wajen fitar da cikakken tsarin tattalin arzikin daji na Najeriya, da ake sa ran zai samar da kuɗaɗen shiga har dala biliyan biyu ($2bn), haɓaka tattalin arziki ga kowa da kowa, da kuma gyara fannin don bunƙasar ƙasa."

Duba hotunan taron a nan kasa:

Tinubu ya saka labule da Kwankwaso a Villa

A baya, Legit Hausa ta ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya gana da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a fadar Aso Rock.

Ganawar da aka yi a ranar 9 ga watan Yunin 2023, ita ce ganawar farko da Tinubu ya yi da Kwankwaso tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Kwankwaso, wanda tsohon gwamnan Kano ne, yana daga cikin fitattun ‘yan takara da suka fafata da Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga Fabrairu, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com