Kwankwaso Ya Isa Fadar Shugaban Kasa Taron da ake Sa Ran Tinubu zai Halarta
- Tsohon gwamna, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya isa fadar shugaban kasa domin halartar babban taron tattalin arziki a Najeriya
- Taron yana gudana ne karkashin jagorancin fadar shugaban kasa tare da hadin gwiwar NatureNews da WEN Synergies
- Masana, masu zuba jari, da jami’an gwamnati za su taru domin tattauna hanyoyin raya dajin Najeriya mai darajar Dala biliyan 2
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A ranar Litinin, 21 ga Yuli, 2025, tsohon dan takarar shugaban kasa kuma jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya isa fadar shugaban kasa, Aso Rock, Abuja.
Zuwan shi fadar Aso Villa yana da nasaba da halartar babban taron kasa kan tattalin arzikin dajin Najeriya.

Source: Facebook
Legit ta hango Kwankwaso a fadar shugaban kasa ne a cikin wani bidiyo da hadimin shi, Saifullahi Hassan ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An shirya taron ne a dakin taro na Banquet Hall a fadar shugaban kasa domin lalubo hanyoyin raya dajin kasar cikin inganci.
An shirya babban taron ne bisa hadin gwiwar NatureNews da WEN Synergies, tare da amincewar fadar shugaban kasa ta hannun kwamitin shugaban kasa kan tattalin arziki da kudi (PreCEFI).
Shugabannin da za su halarci taron
Ana sa ran shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da mataimakinsa, Kashim Shettima, za su halarci taron domin nuna cikakken goyon bayansu.
Rahoton Nature News ya nuna cewa hakan zai iya kara wa taron karfi da muhimmanci wajen fitar da sababbin tsare-tsare.
Taron zai tattaro ministoci, masu zuba jari, masana harkar muhalli, da wakilan kungiyoyin fararen hula domin tattauna hanyoyin da za a bi wajen amfana da albarkatun daji.
Haka zalika kwararru na duniya a fannin daji da tattalin arziki za su gabatar da jawabai masu muhimmanci.
Yadda taron zai habaka tattalin Najeriya
WEN Synergies ya bayyana cewa akwai muhimman fannoni guda shida da za su inganta tattalin arzikin daji da suka hada da tafiyar da daji cikin tsari da karfafa bincike da horo.
A cewar rahoton kamfanin, wadannan matakai za su taimaka wajen samar da ayyukan yi, kare muhalli, da kara habaka tattalin arzikin kasa.

Source: Twitter
Manufar taron da za a yi a Aso Villa
Ana sa ran taron zai haifar da manufofi da matakan aiwatarwa da za su taimaka wajen inganta tsarin daji.
Idan aka dauki lokaci, ana sa ran hakan zai kai ga karuwar ayyukan yi, raya yankunan karkara, da zuba jari ta hanyoyi da dama.
Manufar karshe ita ce daidaita tattalin arziki da sauyin yanayi, da karfafa dasa itatuwa da gwamnatin tarayya ke yi a fadin kasa.
An bayyana cewa wannan tsarin zai kara wa Najeriya karfi wajen saukaka tasirin canjin yanayi da ake fuskanta a duniya.
Kwankwaso ya ziyarci iyalan Buhari
A wani rahoton, kun ji cewa jagoran NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Kwankwaso ya ziyarci iyalan marigayi Muhammadu Buhari.
Sanata Rabiu Kwankwaso ya gana da sarkin Daura a fadar shi domin yi masa ta'aziyya kafin daga bisani ya wuce gidan tsohon shugaban kasar.
Ziyarar da Kwankwaso ya kai ranar Asabar ta rufe bakin wadanda suke sukar shi saboda rashin ganin shi wajen ta'aziyya ko jana'izar Buhari.
Asali: Legit.ng

