Amfanin ‘ya’yan itatuwa 10 wadanda ya kamata ku sani

Amfanin ‘ya’yan itatuwa 10 wadanda ya kamata ku sani

‘Ya’yan itatuwa nada matukar amfani saboda haka yake da kyau da manya da yara su mayar dashi abincinsu nay au da kullun don Karin lafiya.

‘Ya’yan itatuwa na amfani sosai a jikin dan adam shiyasa yake da kyau a ringa kalaci dasu, sannan ya kasance ka ajiyesu a gidanka a ko yaushe.

Yara yanzu sunfi cin abinci wadanda akayi da filawa wanda kuma bashida sinadarai na Karin lafiya a cikinsu sannan kuma suna da barazana ga lafiyar yaran mu a nan gaba, sakamakon abubuwan da aka hadasu dashi, kamar su filawa, sikari, kala da suransu.

Amfanin ‘ya’yan itatuwa 10 wadanda ya kamata ka sani
Amfanin ‘ya’yan itatuwa 10 wadanda ya kamata ka sani

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya nada Keyamo da wasu 6 a matsayin mambobin hukumar NDIC

Abubuwa 10 masu muhimmanci dayasa yake da kyau ka ringa cin ‘ya’yan itace

1. Cin ‘ya’yan itatuwa na kare ka daga kamuwa da cuta

2. ‘Ya’yan itatuwa na kara maka karfin jiki

3. Ruwan dake cikin ‘ya’yan itatatuwa na sanya laushin fata da kuma ruwan jiki

4. Duk ‘ya’yan itatuwa na da sinadarai wadanda ke kara kwayoyin halittar jiki

5. ‘Ya’yan itatuwa na rage kitsen da kiba a jikin mutum

6. ‘Ya’yan itatuwa na karawa jikin dan adam sinadaran Vitamins da Minerals

7. ‘Ya’yan itatuwa na sa jikin mutum ya ringa haske

8. ‘Ya’yan itatuwa na kara kaifin kwakalwa

9. ‘Ya’yan itatuwa na kara karfin jiki da lafiya

10. ‘Ya’yan itatuwa na sanya ‘yan cikinka su zauna lafiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng