Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda Ya Yi Hatsari, An Ji Halin da Yake Ciki
- Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa ya gamu da hatsarin mota a kan titin Daura zuwa Katsina da yammacin yau Lahadi
- Mai magana da yawun gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed ya ce hatsarin ƙarami ne kuma Gwamna Raɗɗa na cikin ƙoshin lafiya
- Duk da dai ba a bayyana abin da ya haddasa hatsarin ba, Ibrahim Kaula ya ce Malam Dikko bai ji wani mummunan rauni a hatsarin ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Rahotannin da muke samu daga jihar Katsina na nuna cewa gwamnan jihar, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya yi hatsarin mota a hanyar Daura zuwa Katsina.
Gwamnatin Katsina ta tabbatar da aukuwar lamarin, tana mai cewa hatsarin ƙarami ne kuma mai girma gwamna yana cikin ƙoshin lafiya.

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan Katsina, Ibrahim Kaula Muhammed ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a daren Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane hali gwamnan jihar Katsina ke ciki?
Ibrahim ya bayyana cewa Gwamna Raɗɗa ya tsira, bai samu wani rauni mai tsanani a hatsarin ba, kuma yana cikin ƙoshin lafiya.
"Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya gamu da wani ƙaramin hatsarin mota da yammacin yau a kan hanyar Daura zuwa Katsina, yayin da yake gudanar da ayyukan gwamnati domin hidimar al’umma.
"Muna farin cikin tabbatar wa da jama’a cewa Gwamna Radda na cikin koshin lafiya kuma yana cikin yanayi mai kyau, ba tare da samun wani rauni mai tsanani ba.
"Gwamna Radda na cikin kwarin gwiwa, kuma ya bayyana godiyarsa ga Allah Maɗaukakin Sarki bisa kariyar da ya ba shi, da kuma godiya ga al’ummar Katsina da duk masu fatan alheri bisa addu’o’insu da nuna damuwarsu.
- Ibrahim Kaula Mohammed.

Source: Facebook
Me ya haddasa hatsarin Gwamna Raɗɗa?
Majiyoyi daga yankin sun nuna cewa Gwamna Dikko na tare da shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Katsina a cikin motar lokacin da hatsarin ya faru.
Gwamnatin Katsina ba ta bayyana ainihin abin da ya haddasa hatsarin ba zuwa yanzu, sai dai ance tuni aka garzaya da Malam Dikko Raɗda zuwa Asibiti a Daura.
Tuni dai al'ummar jihar Katsina suka fara yiwa gwamnan addu'o'in kariya da kuma tsarin Allah SWT daga faruwar irin wannan al'amari a nan gaba.
Jaridar Mobile Media Crew ta bayyana cewa an sallami Gwamna Dikko Raɗɗa daga asibiti a Daura sakamakon babu wani rauni mai tsanani a tattare da shi.
An ba Gwamna Radda lambar yabo
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya lashe lambar yabo ta gwamnan da ya fi kowane aiki a shekarar 2025.
An karrama Gwamna Radda ne bisa namijin ƙoƙarin da yake yi wajen sauya Jihar Katsina ta fuskar inganta ababen more rayuwa, ilimi, lafiya, tsaro da ƙarfafa tattalin arziki.
Gwamnan ya ce ya sadaukar da wannan kyauta ga jajirtattun mata, matasa masu buri, ma’aikata masu himma da kuma daukacin al’ummar Jihar Katsina.
Asali: Legit.ng

