Za a Iya Samun Matsala a Zaɓe, 'Yan Bindiga Sun Harbi Ɗan Takarar Gwamnan PDP a Abuja

Za a Iya Samun Matsala a Zaɓe, 'Yan Bindiga Sun Harbi Ɗan Takarar Gwamnan PDP a Abuja

  • ‘Yan bindiga sun harbe dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Abuja yayin da aka garzaya da shi asibiti domin tiyata
  • Yan bindiga sun kai harin ne kan jigon PDP, Jude Ezenwafor, a kusa da Wuse 2, Abuja ranar Juma’a da dare
  • Ezenwafor ya ce lamarin ya faru ne lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gida, kuma yanzu yana asibiti domin a cire harsashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Wasu yan bindiga sun kuskuri jigon PDP a jihar Anambra da ke Kudu masu Gabashin Najeriya.

Maharan sun kai harin ne kan dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, a zaben jihar Anambra da za a gudanar a watan Nuwambar shekarar 2025.

Yan bindiga sun farmaki dan takarar gwamna a PDP
'Yan bindiga sun harbi dan takarar gwamnan PDP a Anambra. Hoto: Jude Ezenwafor.
Source: Facebook

'Yan bindiga sun bindige jigon PDP a Abuja

Kara karanta wannan

'Zai yi wahala Obi ya yi shugaban kasa,' Hadimin Buhari ya yi martani ga Obidients

Rahoton Vanguard ya ce Jude Ezenwafor, ya tsira daga yunkurin kashe shi bayan an harbe shi da bindiga a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne yayin da Ezenwafor ke kwance a wani asibiti mai zaman kansa a Abuja inda za a yi masa tiyata.

Ezenwafor ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai da safiyar Asabar cewa lamarin ya kusa hallaka shi.

Jigon PDP ya magantu kan harin 'yan bindiga

Ya ce an tare shi da bindiga a kusa da Wuse 2 da daddare ranar Juma’a yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa gida daga wani taro.

Ya ce:

“Ina cikin asibiti a yanzu. Likitoci na kokarin yi min tiyata domin su cire harsasai daga jikina."
Yan sanda sun yi magana bayan harbin jigon PDP
Yan bindiga sun farmaki dan takarar gwamnan PDP a Abuja. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Facebook

Jigon PDP da wasu sun samu raunuka

'Dan takarar na PDP ya ce wasu mutane biyu da ke tare da shi lokacin harin suma an harbe su wanda suke ci gaba da karbar kulawa a asibiti.

Har yanzu ba a san musabbabin harin ba, haka kuma ba a gane wadanda suka kai harin ba, yayin da rundunar ‘yan sanda na ci gaba da bincike, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Mamakon ruwan sama ya jawo ambaliya a gari, mutane 54 sun mutu

Yan bindiga sun sha kai hare-hare kan jiga-jigan siyasa a yankunan kasar da kuma sauran al'umma musamman a yankin Arewa da wasu bangaren Kudancin Najeriya.

Martanin da yan sanda suka yi a Abuja

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar yan sanda da ke birnin Abuja, SP Josephine Adeh, ta shaidawa cewa:

“Ban sani ba. Babu wanda ya sanar da ni.”

A gefe guda kuma, wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP sun ce lamarin na iya yin tasiri kan shirye-shiryen kamfen din jam’iyyar, gwargwadon irin raunin da Ezenwafor ya ji da kuma lokacin da zai warke.

'Yan bindiga sun kashe tsohon shugaban PDP

Mun ba ku labarin cewa yan bindiga sun hallaka tsohon shugaban jam'iyyar PDP a jihar Benue da ke yankin Arewa ta Tsakiya.

Miyagun ƴan bindigan sun kai farmakin ne kan shugaban shugaban na PDP a ƙaramar hukumar Tarka a daren ranar Juma'a 20 ga watan Yunin 2025.

Rundunar ƴan sandan jihar Benue ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce ta fara farautar wanda ake zargi da kitsa kai harin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.