Kwana Ya Ƙare: Daga zuwa Taimakon Ƴan Uwansu Musulmi, Matasa 4 Sun Rasu a Kano

Kwana Ya Ƙare: Daga zuwa Taimakon Ƴan Uwansu Musulmi, Matasa 4 Sun Rasu a Kano

  • Matasa huɗu sun rasa rayukansu a wata magudanar ruwa da aka tsohe saboda aikin layin dogo da ake yi a yankin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a Kano
  • Hukumar kwana-kwana ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawunta, Saminu Yusuf
  • Ya ce bayanan da suka tattara sun nuna cewa mutum biyu sun shiga ruwan ne domin iyo amma suka nutse, wasu ƙarin biyu suka shiga ceto su

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Rahotanni sun tabbatar da mutuwar mutane huɗu duka matasa sakamakon nutsewa a wata magudanar ruwa da aka toshe a jihar Kano.

Lamarin dai ya faru ne a kauyen Zangon Kaya, da ke cikin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan Buhari, Bola Tinubu zai je jihar Kano ta'aziyyar Aminu Dantata

Matasa 4 sun rasa rayukansu a ruwa a jihar Kano.
An tabbatar da mutuwar mutum 4 a magudanar ruwa a jihar Kano Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sunayen matasan da suka mutu a Kano

Jaridar Leadership ta rahoto cewa matasan da suka rasa rayukansu sun haɗa da Nasirudden Tasi’u mai shekara 25, da Bashir Sani mai shekara 28.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sune, Yakubu Muhd mai kimanin shekara 22 a duniya da kuma Usman Ubale ɗan kimanin shekara 26.

Mai magana da yawun Hukumar Kwana-kwana ta Jihar Kano, Saminu Yusif, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Kano ranar Asabar.

A cewar Saminu, hukumar ta samu kiran gaggawa misalin ƙarfe 1:48 na rana daga wani Rabiu Yusif wanda ya sanar da su cewa wasu mutane sun fada cikin ruwan tafkin da ba ya tafiya.

Yadda mutum 2 suka shiga ceto ƴan uwansu

Saminu Yusif ya bayyana cewa, magudanar ruwan ta cika ne da ruwa sakamakon aikin ginin layin dogo da ake yi a yankin.

Ya ce da farko, mutum biyu daga cikin waɗanda suka mutu sun shiga domin yin iyo da wanka, amma suka makale, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jagoran yan ta'adda ya shiga hannu, ya fara ambato abokan hulɗarsa bayan ya ji matsa

Ya ƙara da cewa sauran mutane biyu kuma sun shiga ruwan ne da nufin taimakon waɗanda suka maƙale su ceto su, amma su ma suka makale.

"Kafin isowar jami’anmu, mutanen da ke yankin sun sami damar ciro biyu, sannan tawagar ceto ta kwana-kwana ta ciro sauran guda biyu daga cikin ruwan,” in ji shi.
Abdullahi Haruna Kiyawa, kakakin ƴan sandan Kano.
An ciro gawarwakin matasa 4 da suka mutu a ruwa a Kano Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

An miƙa wa ƴan sanda gawarwakin matasan

Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar kwana-kwana ya ce duk waɗanda aka ciro ba su a cikin hayyacin kansu, kuma daga bisani an tabbatar da mutuwarsu.

Sanarwar ta ƙara da cewa an mika gawarwakin zuwa hannun jami’in rundunar ‘yan sanda, SP Abdulkadir M. Albasu na caji ofis din ‘yan sanda na Dawanau.

An yi hasashen saukar ruwan sama a Kano

A wani labarin, kun ji cewa hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama mai yawa da tsawa a Arewacin Najeriya daga Juma’a zuwa Lahadi.

Kano, Kaduna da Abuja na cikin yankunan da hukumar ta yi hasashen za a samu ruwa mai ƙarfi, inda ta gargaɗi gwamnati ta jama'a su shirya don gujewa ambaliya.

Wannan dai na zuwa ne yayin da daminar bana ta kankama a Arewacin Najeriya, sai dai ana gudun yawan ruwa mai ƙarfi na jawo haɗarin ambaliya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262