An Yi Taron Musulmai na Duniya a Ingila, Sarkin Musulmi Ya Wakilci Najeriya

An Yi Taron Musulmai na Duniya a Ingila, Sarkin Musulmi Ya Wakilci Najeriya

  • Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya halarci taron shugabannin Musulmi na duniya a Oxford, inda ya bukaci inganta zaman lafiya
  • Taron na kwana biyu ya zo ne a matsayin bikin cika shekara 40 da kafuwar cibiyar nazarin addinin Musulunci ta Oxford
  • Taron ya samu halartar manyan shugabanni ciki har da Sarki Charles III, tsohon shugaban Turkiyya Abdullah Gul da yarima Turki Al Faisal

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

England – Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya bukaci shugabanni da al’umma su rungumi zaman lafiya a matsayin hanyar samun hadin kai da zaman lafiya a duniya.

Sarkin Musulmi ya bayyana hakan ne yayin halartar wani taro na shugabannin Musulman duniya da aka gudanar a cibiyar nazarin addinin Musulunci ta Oxford a Ingila.

Kara karanta wannan

London Clinic: Abubuwan mamaki game da asibitin da Muhammadu Buhari ya rasu

Sarkin Musulmi a taron Musulunci a Oxford.
Sarkin Musulmi a taron Musulunci a Oxford. Hoto: @cbabdullahgul
Source: Twitter

Rahoton Voice of Nigeria ya tabbatar da cewa fitattu daga cikin shugabannin duniya sun samu halartar taron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron da ya gudana na tsawon kwana biyu, ya zo daidai da cika shekaru 40 da kafuwar cibiyar, tare da gudanar da babban taron shekara-shekara na kwamitin amintattu na cibiyar.

Yadda Sarki Charles III ya bude taron

Sarki Charles III ne ya bude taron a hukumance ranar Alhamis, inda manyan baki suka halarta daga sassa daban-daban na duniya.

Cikin manyan bakin da suka halarci taron har da tsohon shugaban ƙasar Turkiyya, Abdullah Gul, yarima na Saudiyya Turki Al Faisal.

Haka zalika Sarkin Perak na Malaysia, Nazrin Shah ya halarci taron kuma dukkansu mambobi ne na kwamitin amintattu na cibiyar.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, wanda shima mamba ne na wannan kwamiti, ya samu rakiyar Sarkin Fadansa, Alhaji Kabir Aminu Tafida, a tafiyar zuwa Ingila.

Sarki Charles tare da Fafaroma da ya rasu a bana.
Sarki Charles tare da Fafaroma da ya rasu a bana. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sarkin Musulmi ya yi jawabi kan zaman lafiya

A jawabin da ya gabatar bayan taron, Sarkin Musulmi ya jaddada bukatar zaman lafiya da tattaunawa musamman a nahiyar Afirka.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Za a yi wa shugaba Buhari addu'a a coci ranar Lahadi

Rahoton Channels TV ya nuna cewa ya ce:

“Ya kamata duniya gaba ɗaya, musamman Afirka, su rungumi zaman lafiya da tattaunawa a ko da yaushe domin samar da daidaito da fahimta tsakanin al’umma.”

Ya ƙara da cewa addinin Musulunci na koyar da zaman lafiya, don haka ya kamata a ci gaba da amfani da koyarwar Musulunci wajen tabbatar da fahimtar juna da haɗin kai.

Manufofin cibiyar Musulunci ta Oxford

Cibiyar Musulunci ta Oxford da wasu manyan manufofi da suka haɗa da inganta fahimta tsakanin addinai da al’adu daban-daban.

Haka kuma tana maida hankali kan ci gaban matasan Musulmi a Birtaniya, tare da bayar da tallafin karatu, bincike da batutuwan muhalli da harkokin kuɗi a Musulunci.

Taron ya kasance wata dama ta musamman ga shugabannin Musulmi da sauran masu ruwa da tsaki su tattauna kan hanyoyin da za a inganta zaman lafiya a duniya.

Dan Dahiru Bauchi ya je Turkiyya

A wani rahoton, kun ji cewa Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya kai wata ziyara kasar Turkiyya.

Kara karanta wannan

An fadawa Tinubu abu 1 da Najeriya ke bukata bayan mutuwar Buhari a London

Sayyadin ya bayyana cewa an dade ana neman shi ya kai ziyarar amma Allah bai ba shi ikon hakan ba sai a bana.

Ibrahim Dahiru Bauchi ya bayyana cewa mahaifinsu ba shi da akidar cewa Sheikh Ibrahim Inyass na da karamar bayyana a bango.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng