Buhari, Sheikh Abubakar Gumi da Wasu Jagororin Najeriya 6 da Suka Rasu a Birnin Landan
A ranar Lahadi da ta gabata ne Allah ya yi wa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari rasuwa a wani asibiti a birnin Landan na ƙasar Birtaniya.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Wannan dai ba shi ne karo na farko da wani jagoran al'umma a Najeriya ya rasu a ƙasar Birtaniya da ke nahiyar Turai ba.

Source: Facebook
Tribune Nigeria ta ruwaito cewa rasuwar Buhari ta ƙara haddasa ce-ce-ku-ce kan yadda manya ke tsallake asibitocin Najeriya suna tafiya ƙasashen ƙetare.
Haka kuma ƴan Najeriya sun fara nuna damuwa kan tsarin lafiyar Birtaniya duba da yadda jagororinsu da suka rasu a asibitocin Landan da wasu wurare a ƙasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabanni 8 a Najeriya da suka rasu a Landan
Sakamakon haka, Legit Hausa ta tattaro maku shugabannin al'umma takwas da suka tafi neman lafiya a Birtaniya amma sai gawarsu aka dawo da ita gida.

Kara karanta wannan
Najeriya ta yi martani ga Turkiyya kan zargin bullar sabuwar kungiyar yan ta'addan FETO
1. Muhammadu Buhari (Shekara 82):
Tsohon Shugaban Ƙasa a Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi mulkin farar hula daga 2015 zuwa 2023, sannan kuma ya shugabanci ƙasar a matsayin soja daga 1983 zuwa 1985.
Buhari ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025 a wani asibiti da ke birnin London bayan fama da rashin lafiya.
2. Sheikh Abubakar Gumi ( Shekara 70)
Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, babban malamin addinin musulci ne kuma alkai a Najeriya, ya yi fice wajen bin tafarkin Sunnah.
An haife shi a garin Gummi da ke jihar Sakkwato a 1922 kuma ya rasu ne a birnin Landan na ƙasar Ingila ranar 11 ga watan Satumba, 1992.
3. Oluyemi Adeniji (Shekara 83)
Oluyemi Adeniji ya riƙe kujerar ministan harkokin wajen Najeriya lokacin mulkin Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo.
Ya wakilci Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya kuma ya jagoranci ayyukan zaman lafiya a Afirka. Ya rasu a wani asibiti da ke London.

Kara karanta wannan
Hoton yadda Aisha Buhari ta rungume tutar da aka lulluɓo gawar mijinta ya ja hankali
4. Ifeanyi Ubah (Shekara 53)
Ifeanyi Ubah Sanata ne da ya taba wakiltar Anambra ta Kudu kuma attajiri wanda ya kafa kamfanonin jirgin ruwa, man fetur da otal-otal.
Sanatan ya rasu ba zato ba tsammani a birnin Landan, wasu majiyoyi sun ce ya mutu ne yayin da ya je a masa tiyata kan rashin lafiyar da ba a bayyana ba.

Source: Facebook
5. Clement Nyong Isong (Shekara 78)
Clement Nyong Isong ya kasance tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) kuma tsohon gwamnan jihar Kuros Riba,
Ya samu kulawa ta musamman a wani asibiti a Landan kuma ya rasu a shekarar 2000 bayan gajeruwar rashin lafiya.
6. Sheikh Isyaka Rabiu (Shekara 93)
Sheikh Isyaka Rabiu babban malami ne kuma fitaccen ɗan kasuwa wanda ya bayar da gudunmawa ga al’umma a jihar Kano da ƙasa baki ɗaya.
Ya gina makarantu da asibitoci a jihar Kano. Khalifa Isyaka Rabiu ya rasu a wani asibiti da ke Landan bayan doguwar jinya.
7. Oba Okunade Sijuwade (Shekara 85)
Babban sarki ne mai ƙima a yankin Yarbawa. An san shi da ƙoƙarinsa na haɗa kan mutane.
Basaraken ya rasu a wani asibiti a birnin Landan na ƙasar Birtaniya a shekarar 2015.
8. Alex Ekwueme (Shekara 85)
Shi ne Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa na farko da aka zaɓa a tarihin Najeriya karkashin mulkin Shehu Shagari.
Alex Ekwueme ya sha gwagwarmaya wajen samar da tsarin gwamnatocin jihohi 36 da kuma ci gaban dimokuraɗiyya. Ya rasu a wani asibiti a Landan a 2017.
Yadda Shugaba Buhari ya hango mutuwarsa
A wani labarin, kun ji cewa tsohon kakakin shugaban ƙasar ya ce Muhammadu Buhari ya taɓa faɗa masa cewa bayan ya bar mulki, zai koma gida ya jira lokacin mutuwarsa.
Femi Adesina ya ce wasu na mamakin yadda mutuwar dattijo ɗan shekara 82 ta girgiza su, yana mai cewa Buhari shugaba ne na gari da zai wahala a maye gurbinsa.
Adesina ya ce ba zai taɓa manta lokacin da ya shafe tare da tare da Baba Buhari, wanda ya kira ubangida, aboki kuma shugaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
