Bango ya fadi: Allah ya yiwa Khalifa Sheikh Isyaka Rabi'u rasuwa
Allah ya yiwa shahararren malami kuma attiji, Sheikh Khalifa Isyaka Rabi'u, rasuwa da yammacin yau, Talata. Marigayin ya rasu ne a birnin Landan inda yake zaman jinya a wani asibiti. Shikh Rabi'u shine mahaifi ga Alhaji. Abdulsamad Isyaka Rabi'u, mai kamfanonin rukunin BUA.
Khalifa Isyaka Rabi'u shine shugaban darikar Tijjaniya a jihar Kano.
Ya zuwa yanzu iyalin sa basu sanar da lokacin da za a gudanar da jana'izar sa ba domin har yanzu ba a kawo gawar sa Najeriya ba.
DUBA WANNAN: Hanyoyi biyu da motsa jiki ke haddasa mutuwa
Kafin mutuwar sa Shekh Rabi'u na daga cikin manyan dattijan jihar Kano da suka rage a raye. Duk da Allah ya karbi ran sa, Sheikh Rabi,u, ya shiga sahun dattijan kano da suka dade a duniya, suka ga abubuwa da dama a jihar Kano da ma Najeriya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng