An Shiga Firgici a Katsina: Ƴan Bindiga Sun Sace Wani Kansila kuma Ƙanin Ciyaman
- Wani kansila a Katsina, Buhari Aliyu, da abokinsa Nura Kaura sun fada hannun ’yan bindiga a kan hanyarsu ta komawa Daudawa
- Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa ’yan bindigar sun sace su ne a hanyar Funtua zuwa Sheme, ba a cikin garin Daudawa ba
- Ana kuma zargin cewa wani ke bibiyar motar kansilan yana baiwa ’yan bindiga bayani, yayin da har yanzu ba a tuntubi iyalansa ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - 'Yan bindiga sun yi garkuwa da kansilar gundumar Daudawa da ke karamar hukumar Faskari, jihar Katsina a ranar Litinin 14 ga watan Yulin 2025.
An sace kansilan mai suna Buhari Aliyu Daudawa tare da abokinsa Nura Kaura Wanzan da wasu mutane a hanyarsu ta komawa Daudawa daga Funtua.

Source: Facebook
An yi garkuwa da kansila a Katsina
Wani mazaunin garin Daudawa, Mallam Muhammad Salihu ya shaidawa Legit Hausa cewa 'yan bindigar sun yiwa kansilar kwanton bauna a yankin Dankama da ke hanyar Funtua zuwa Sheme.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mallam Muhammad ya karyata rahotannin da wasu kafafen watsa labarai ke yadawa cewa har cikin garin Daudawa 'yan bindigar suka shiga suka tafi da Hon. Buhari Aliyu.
"Ba cikin Daudawa suka dauke shi ba. Nan wajen burtsatse suka dauke shi, kwarin nan na wajen garin Dakamawa suka tare su, suka tafi da su,"
- A cewar Mallam Muhammad.
Mazaunin garin Daudawan ya ce suna zargin wani 'infoma' (mai ba 'yan bindiga bayanai) ne ya rika bibiyar motar kansilan, yana ba miyagun bayanai har suka kama shi.
Kanin ciyaman din Faskari aka sace
Mallam Muhammad ya kara da cewa:
"Wallahi wani ne ke binsa, don har waya ma ya kira, ya ce akwai wanda yake bibiyarsu. Amma ya ce a kyale shi har sai sun ga yadda ta kwaranye, in ya so sai a gano wanene shi."
Ya ce akwai wasu 'yan Daudawa da aka yi garkuwa da su a kwanan baya, amma an sako su jiya Laraba bayan biyan sama da N6m da sabon babur.
Hon. Buhari Aliyu ya lashe zaben kansila a gundumar Daudawa karkashin APC a zaben ciyamomi da kansiloli da aka gudanar a jihar Katsina a watan Fabrairun 2025.
Yayansa, wanda suke uba daya, Surajo Aliyu Daudawa shi ne ya lashe shugaban karamar hukumar Faskari a zaben da aka gudanar.

Source: Facebook
Ba a ji daga bakin rundunar 'yan sanda ba
An fahimci cewa har yanzu 'yan bindigar ba su tuntubi iyalan dan siyasar ba, kuma ba a san inda suka kai shi ba tsawon wadannan kwanaki.
Legit Hausa ba ta samu jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu game da wannan lamarin ba har zuwa lokacin wallafa rahoton.
Da wakilin jaridar ya kira kakakin 'yan sandan a waya, sai ya aiko masa da sakon cewa 'ba zai iya yin magana a yanzu ba,' kuma bai maido da amsar sakon da aka aika masa ba.
Mutanen Faskari sun kama 'yan bindiga
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindigar da suka kai hari yankin Tafoki da ke Faskari, jihar Katsina sun gamu da fushin jami’an tsaro.
A yayin musayar wuta da masu tsaron garin, wasu daga cikin ’yan bindigar sun samu munanan raunuka kuma suka tsere zuwa daji.
An ruwaito cewa washegari, mazauna garin sun kama wasu daga cikin raunanan ’yan bindigar su uku kuma suka kashe su nan take.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


