Hoton Yadda Aisha Buhari Ta Rungume Tutar da Aka Lulluɓo Gawar Mijinta Ya Ja Hankali
- A ranar Talata, 15 ga watan Yuli 2025, aka birne tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura a jihar Katsina
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya karɓi gawarsa da aka lullube da tutar Najeriya mai fari da kore, kafin daga bisani aka wuce Daura aka masa sutura
- Wani hoton Aisha Buhari, tsohuwar uwargidan shugaban Ƙasa, ɗauke da tutar da aka lulluɓo mijinta ya ja hankalin mutane a kafafen sada zumunta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Daura, jihar Katsina - Bayan kammala sallar jana'iza, an birne marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura a jihar Katsina ranar Talata.
Legit Hausa ta kawo maku rahoton yadda aka yi wa marigayin jana'iza har aka birne shi, inda manyan mutane da dubban al'umma suka halarta don bankwana da shi.

Kara karanta wannan
'Zai yi wahala Obi ya yi shugaban kasa,' Hadimin Buhari ya yi martani ga Obidients

Source: Twitter
Rahoton Vanguard ya nuna cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya halarci jana'izar magabacinsa domin girmamawa da kuma bankwana da abokinsa na siyasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka lulluɓo Buhari da tutar Najeriya
Tun a ranar Lahadi, 13 ga watan Yuli 2025, Allah Ya karɓi ran Buhari a wani asibiti a Landan, duk da har yanzu ba a bayyana taƙamaiman cutar da ta yi ajalinsa ba.
Gawar Buhari da aka ɗauko a makara lulluɓe da tutar Najeriya mai launin fari da kore, ta iso filin jirgin Umaru Musa Yar'adua da ke Katsina da tsakar rana a ranar Talata.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya karɓi gawar a filin jirgin, sannan sojoji suka yi masa faretin girmamawa da harba bindiga, kafin daga bisani aka ɗauki gawar zuwa Daura.

Source: Twitter
Hoton Aisha Buhari ya taɓa zukatan jama'a
Bayan kammala jana'izar, wani hoto da ke nuna tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, cikin wani yanayi na alhini ya jawo hankalin masu amfani da shafukan sada zumunta.
Bashir Ahmad, tsohon hadimin Buhari, ne ya wallafa hoton Aisha cikin yanayi na alhini a shafinsa na X da aka tabbatar da sahihancinsa.
Bashir Ahmad ya wallafa hoton tare da rubutaccen sako mai cewa:
"Duba yadda Aisha Buhari ta rungumi tutar Najeriya da aka nade gawar Janar Buhari da ita bayan Shugaba Bola Tinubu ya mika mata cikin natsuwa."
Abin da ƴan Najeriya ke cewa game da hoton
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin sharhin da aka yi kamar haka:
@Ashabul_Jannaah ta ce:
"Baki ba zai iya bayyana halin da take ciki ba. Ta zama bazawara, ga tuta, da bankwana ga Janar ɗin ƙasa. Allah ya ƙarfafa mata zuciya, ya kuma ba Baba Buhari hutun har abada."
Folashade Aduke ya ce:
"Lokaci ne mai cike da tausayi. Allah Ya jikansa."
@OlabodeAbdul11 ya rubuta:
"Ina mika ta'aziyya ga dukan iyali, abokai, abokan aiki da kuma mutanen Katsina, musamman na Daura.
"Wannan babban rashi ne. Muna addu'ar Allah ya gafarta masa kura-kuransa ya kuma ba shi Aljannatul Firdaus."
Noor ta fara kewar mahaifinta, Buhari

Kara karanta wannan
Buhari: Diyar tsohon shugaban kasa ta fadi halin da ta shiga bayan rasuwar mahaifinta
A wani labarin, kun ji cewa ɗiyar marigayi Muhammadu Buhari, Noor ta bayyana cewa ranta ya sosu matuƙa da ta samu labarin rasuwar mahaifinta.
Noor ta ce mutuwa ta katse duk wasu abubuwa da ta shirya yi da mahaifinta, tana mai cewa ya koma ga mahaliccinsa a lokacin da take buƙatarsa.
Wannan kalamai na Noor sun taɓa zuƙatan ƴan Najeriya, waɗanda tuni suka fara alhinin rasuwar tsohon shugaban ƙasar, wanda aka fi sani da Baba Buhari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
