Jagoran Yan Ta'adda Ya Shiga Hannu, Ya Fara Ambato Abokan Hulɗarsa bayan Ya Ji Matsa

Jagoran Yan Ta'adda Ya Shiga Hannu, Ya Fara Ambato Abokan Hulɗarsa bayan Ya Ji Matsa

  • Dakarun sojojin kasar nan sun kara samu nasara a yaƙin da su ke da yan ta'adda da suka hana mazauna Sakkwato sakat
  • An kama kasurgumin ɗan ta’adda mai suna Abubakar Magaji a Silame, Sakkwato, dauke da bindigar AK-47 da harsasai
  • Magaji ya amsa cewa yana cikin ƙungiyar masu garkuwa da mutane da ke aikata laifuffukan garkuwa da mutane a dajin Silame

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Rundunar ‘yan sanda ta kama wani shahararren ɗan ta’adda mai suna Abubakar Magaji a jihar Sakkwato.

An yi nasarar rama da fitinannen dan ta'addan bayan wani samame da aka gudanar a karamar hukumar Silame.

Sojoji sun kai samame jihar Sakkwato
An kama jagoran yan ta'adda a Sakkwato Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa an cafke Abubakar da bindigar AK-47 mai ɗauke da harsasai 22 a hannunsa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Mamakon ruwan sama ya jawo ambaliya a gari, mutane 54 sun mutu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasarar damke shi ta samu ne bayan da jami'an leken asiri suka samu bayanan sirri, aka kuma gaggauta bibiya har aka kai ga gano shi tare da cafke shi.

An cafke dan ta'adda a Sakkwato

Rahoton ya ƙara da cewa an kama Abubakar ne a ranar 13 ga Yuli, 2025, ta hannun runduna ta musamman mai yaƙi da garkuwa da mutane da ke ƙarƙashin a Sakkwato.

A yayin binciken farko, Magaji ya amsa cewa shi ɗan wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane da ke da hannu a hare-hare da sace-sacen mutane a dajin Silame da kewaye ne.

Bayan bayanan da ya bayar, dakarun tsaro sun kaddamar da wani samame na ceto da kuma kwato makamai a cikin dajin Silame a ranar 16 ga Yuli, 2205.

An fara binciken yan ta'adda a Sakkwato

Wanda ake zargi ya bayyana sunayen wasu ’yan kungiyar guda huɗu da a yanzu haka sun yi layar zana, yayin da dakaru su ka baza komarsu.

Kara karanta wannan

An fadi lokacin da ake sa ran birne Muhammadu Buhari a Daura

A cikin rahotannin da ya bayar, an gano cewa kowannensu na da bindigar AK-47 da suke aikin ta'addanci da ita a garuruwan da ke kusa da Silame.

Sojojin Najeriya sun yi aiki a Sakkwato
Ana bibiyar wasu yan ta'adda a Sakkwato Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Wata majiya daga rundunar tsaro ta tabbatar da cewa an fara bincike da kamo waɗanda suka tsere, tare da yunƙurin kwato sauran makaman da ke hannunsu.

Ana sa ran da bayanan da aka samu, zai taimaka nuna wa dakarun wuraren da yan ta'addan su ke ayyukansu domin a rage mugun iri.

Sakkwato: Gwamnati ta kafa sharudda ga Turai

A baya, mun wallafa cewa gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana wasu sharudda da dole ne shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji, ya cika kafin a kammala yarjejeniyar sulhu da shi.

Mai ba Gwamna Ahmed Aliyu shawara kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Usman mai ritaya, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar kan batun sulhu da Turji.

Gwamnatin ta bukaci Turji da ya fara nuna kwararan alamun gaskiya da amincewa da shirin zaman lafiya ta hanyar sakin mutanen da ke hannunsa a matsayin fursunoni.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng