'Yan Bindiga Sun Sace Mata Sun Dirka Musu Ciki, Wasu Sun Haihu a Daji
- Wasu matan da aka sace daga yankunan Rafi da Shiroro a Jihar Neja a watan Fabrairu 2024, sun dawo gida da tsohon ciki, wasu da jarirai
- Rahotanni sun nuna cewa ana zargin juna biyun da jariran duk na miyagun ‘yan ta’adda da suka kwashe tsawon shekara suna hannunsu ne
- Rundunar 'yan sandan jihar Neja ta bayyana kokarin da ta ke domin cigaba da yaki da 'yan bindiga da ceto mutanen da aka sace a jihar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Neja – Wasu matan da aka sace a Rafi da Shiroro a Jihar Neja a Fabrairu 2024, sun dawo gida makonni kadan bayan 'yan sanda sun ceto su.
Abin tausayi ne ganin cewa daga cikin matan akwai wadanda ke dauke da tsohon ciki wasu kuma suna dauke da jarirai.

Source: Original
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa mutanen yankunan sun bukaci jami'an tsaro da hukumomi su ba matan kulawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka ceto matan a jihar Neja
Mata guda hudu daga cikin wadanda aka dawo da su sun fito ne daga cikin wata tawaga ta mata 25 da suka fito daga Allawa a kan hanyar Pandogari-Allawa.
Bayan dawowa daga kasuwnci suka shiga wasu motocin haya da ‘yan ta’adda suka dauka daga Palu‑Waya a kewayen Shiroro.
Wani rahoto ya bayyana cewa sun yi niyyar kai su Kebbi ne ko kuma Borgu amma a yayin da suke Kagara, daya daga cikinsu ta nemi tsayawa saboda ta bukaci zuwa bayan gida.
Da suka tsaya sai ta yi ihu, hakan ya kai ga tona asirin 'yan ta'addan tare da kama direban motar, hakan ya kai ga kubutar da su gaba daya.
An samu matan da aka sace da ciki
Wata majiya daga Allawa ta tabbatar da cewa wasu daga cikin ‘yan matan da aka dawo da su suna da tsohon ciki.
Majiyar ta ce matan da dama sun nuna damuwa bisa zargin an yi musu aure dole yayin zaman da suke a hannun masu garkuwa, wanda hakan ya sa wasu ke dauke da jarirai.
Matakan ‘yan sanda da halin da ake ciki
Kakakin ‘yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar a wata sanarwa cewa an ceto mata da yara 35 ciki harda mata 24 da aka nufi kai su Kebbi.
SP Wasiu Abiodun ya bayyana cewa an kai su cibiyar lafiya domin a duba su sannan aka mayar da su ga iyalansu.

Source: Facebook
An yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su ba su kulawa ta musamman domin tabbatar da sun dawo cikin hayyacinsu yadda ya kamata.
'Yan ta'addan FETO sun shigo Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin kasar Turkiyya ta ce 'yan ta'addan kungiyar FETO ta shigo Najeriya.
Turkiyya ta ayyana kungiyar a matsayin 'yar ta'adda a shekarun baya bayan wani yunkurin juyin mulki da aka zarge ta da yi.
Kasar Turkiyya ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta tashi tsaye wajen yaki da 'yan ta'addan domin hana su yaduwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

