NiMet: Kano, Yobe da Jihohi 30 da Ake Sa Ran Ruwan Sama Zai Sauka Ranar Alhamis
- NiMet ta fitar da hasashen yanayi na yau Alhamis, 17 ga Yuli, 2025, inda ta nuna yiwuwar samun ruwan sama mai yawa a Arewa
- Wasu jihohin Arewa za su fuskanci tsawa da ruwan sama mai matsakaicin karfi, yayin da za a samu ruwa kaɗan a Kudancin kasar
- Hukumar hasashen yanayin ta shawarci jama'a da direbobi su yi taka tsantsan saboda yiwuwar ambaliya, da hatsarin ababen hawa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta fitar da hasashen yanayi na yau Alhamis, 17 ga Yulin 2025.
Rahoton ya nuna cewa wasu jihohi za su fuskanci ruwan sama mai yawa, yayin da wasu za su sami ruwan sama kaɗan.

Source: Original
Hukumar NiMet ta fitar da rahoton hasashen yanayin ne a shafinta na X a ranar 16 ga Yulin 2025, kuma ta ce rahoton zai yi aiki ne daga karfe 12:00 na safiya zuwa karfe 11:59 na dare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hasashen yanayi a jihohin Arewa
Da safiyar yau:
Ana sa ran sararin samaniya zai hade da hadari, amma za a samu bullar rana kaɗan a mafi yawan sassan yankin.
Akwai yiwuwar samun ruwan sama da tsawa mai yawa a sassan jihohin Sokoto, Katsina, Kano, Zamfara, da Kebbi.
Da yamma zuwa dare:
Ana sa ran samun ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi tare da tsawa a sassan jihohin Borno, Jigawa, Yobe, Kano, Katsina, Kaduna, Bauchi, Gombe, Taraba, da Adamawa.
Hasashen yanayi a Arewa Tsakiya
Da safiyar yau:
Ana sa ran sararin samaniya zai hade da hadari, amma za a samu bullar rana kaɗan a mafi yawan sassan yankin.
Da yamma zuwa dare:
Ana sa ran ruwan sama zai sauka a sassan babban birnin tarayya (FCT), jihohin Plateau, Nasarawa, Benue, Kogi, Kwara, da Neja.
Hasashen yanayi a jihohin Kudu
Da safiyar yau:
Ana sa ran hadari zai hadu sosai sannan a samu ruwan sama kaɗan a sassan jihohin Ekiti, Edo, Delta, Cross River, da Akwa Ibom.
Da yamma zuwa dare:
Ana sa ran ruwan sama kaɗan a sassan jihohin Imo, Abia, Ebonyi, Edo, Anambra, Enugu, Bayelsa, Delta, Rivers, Cross River, da Akwa Ibom.

Source: Original
Shawarwari da gargadi daga NiMet
An shawarci jama’a da su yi taka tsantsan domin akwai yiwuwar ambaliyar ruwa, hatsarin mota saboda tsawa, iska da kuma ruwa mai ƙarfi.
Hukumar ta kuma shawarci direbobi da su guji yin tuƙi a lokacin ruwan sama mai yawa don gujewa hatsarori.
Hakanan, a guji neman mafaka a ƙarƙashin bishiyoyi yayin guguwa saboda yiwuwar faɗuwar rassan bishiyoyin.
Hukumar ta kuma shawarci kamfanonin jiragen sama da su sami rahotannin yanayi na filayen jiragen sama da bayanan jirgi daga NiMet don tafiye-tafiye cikin aminci.
Malamai sun kira sallar rokon ruwa a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa, malaman addinin Musulunci a Kano sun yi kira ga al'umma da su fito sallar neman ruwan sama, sakamakon ƙarancin ruwan da ake fuskanta.
Sheikh Ibrahim Khaleel, shugaban majalisar malamai ta jihar Kano ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Legit Hausa ta fahimci cewa Musulmi sun fito sallar roƙon ruwan tun a ranar ranar Asabar da ta gabata domin neman taimakon Allah game da daminar bana.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


