Gwamnati za Ta Buɗe Makarantun da Ganduje Ya Rufe, Za a Kashe sama da N3bn a Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya amince da kashe Naira biliyan 3.03 domin gyaran makarantu 13
- Makarantun kwanan, wanda yawancinsu na karkara ne, sun samu matsala ne har ta kai Abdullahi Ganduje ya rufe su
- Sai dai gwamnatin jihar Kano na ganin an yi kuskure, domin hakan ya kara jefa ɓangaren ilimi a halin ƙaƙanikayi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da kashe sama da Naira biliyan 3.03 domin gyaran gine-gine da sabunta makarantu 13 na kwana a fadin jihar Kano.
Wadannan makarantu dai gwamnatin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ce ta rufe su tun a baya saboda dalilanta.

Source: Facebook
Daily Trust, ta ruwaito cewa wannan bayani na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai ba gwamna shawara kan harkokin yada labarai, Ibrahim Adam, ya fitar.
Kano: Gwamnatin Abba za ta gyara makarantu
Wani mai amfani da shafin X, Tahir Prime, ya wallafa cewa gwamnatin Kano ta kudiri aniyar sake bude wadannan makarantu 13 da ke a wurare daban-daban.
Sanarwar ta bayyana cewa za a yi gyaran ne saboda lalacewar gine-gine da kuma kayan aiki a wadannan makarantu da gwamnatin ke shirin farfado da su.

Source: Facebook
Ibrahim ya ce gwamnatin yanzu ta jajirce wajen farfado da harkar ilimi musamman a yankunan karkara domin tabbatar da ci gaba.
Gwamna Yusuf ya jaddada cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar kyautata ingancin ilimi tare da tabbatar da cewa babu wani yanki na jihar da za a bari a baya.
Kan gyara makarantun, ya ce hakan zai samar da muhalli mai kyau don koyarwa da koyo, tare da mayar da damar karatun kwana ga daliban da ke daga yankunan da ke bukatar tallafi. Ya ce:
Makarantun Kano 13 da Abba zai gyara
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf na shirin gyaran makarantu 13 na kwana da suka hada da na maza da na mata a sassa daban-daban na jihar.
A cewar sanarwar:
“Makarantun kwana da aka amince a gyara su sun hada da: GGSS Unguwar Gyartai, GGSS Gezawa, GGSS Sumaila, GGSS Kwa, GGSS Albasu, GGSS Madobi, GGSS Yar Gaya, GGSS Jogana, GGSS Danzabuwa, Unity College Karaye, GGU Kachako, GGSS Jambaki da GC Tudun Wada.”
Ibrahim Adam ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na cikin damuwa da yadda aka bar bangaren ilimi ba tare da kulawa ba a shekarun baya.
Ya ce musamman halin da wadannan makarantu 13 suka shiga ne ya fi tayar masa da hankali, duba da cewa yawancinsu na karkara su ke.
Gwamnan Kano ya biyawa dalibai kuɗin makaranta
A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Kano, karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta biyan kudin rajistar jarrabawa ga dalibai 3,526 da ke sassan jihar da dama.
Wannan mataki zai baiwa wadannan dalibai damar rubuta jarrabawar kammala sakandare ta NECO da ta Hukumar Nazarin Harshe da Ilimin Addinin Musulunci (NBAIS).
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da daukar nauyin ne bayan daliban sun yi nasarar cin jarrabawar cancanta da ake kira qualifying a makarantunsu a daban-daban.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

