An Yi Babban Rashi: Matar Sarkin Kano Sanusi I da Ƴarsa Sun Rigamu Gidan Gaskiya
- Masarautar Kano ta shiga jimami bayan rasuwar iyalin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I, Yaya Jide da 'yarsa, Goggo Ummahani
- Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammad Sanusi II, ne ya jagoranci sallar jana’izar matan biyu a ranar Laraba, 16 ga Yulin 2025
- Sanusi I ya mulki Kano daga 1954 zuwa 1963, kuma Sanusi II ya fara hawan karagar 2014, sannan ya sake komawa a 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Zuriyar masarautar Kano, musamman ahalin Sarki Sanusi Bayero I, sun shiga cikin jimami bayan rasuwar iyalan Sarkin Kano Sanusi I.
Goggo Ummahani, 'yar Sarkin Kano Sanusi I, wanda ya mulki jihar Kano daga 1954 zuwa 1963 ta rasu.

Asali: Twitter
Diyar Sarki Sanusi I da iyalinsa sun rasu
Wata sanarwa daga shafin Masarautar Kano na X ta nuna cewa Mai Martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sanusi II ne ya jagoranci sallar jana'izar Goggo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, sanarwar ta ce Allah ya karbi rayuwar Yaya Jidde, matar Sarkin Kano Sanusi I, inda aka hada Goggo da Yaya Jidde aka sallace su tare.
Sanarwar ba ta yi bayani game da silar mutuwar tasu ba, la'akari da cewa an yi jana'izarsu tare, amma masarautar ta ce an yi wa matan biyu sutura ne a ranar 16 ga Yulin 2025.
Masarautar Kano ta rahoto cewa:
"Mai Martaba Sarkin Kano Khalifa Dr. Muhammad Sanusi II, ya jagoranci sallar jana’izar Goggo Ummahani Sanusi Bayero 'yar Sarkin Kano Sanusi 1, tare da Yaya Jidde iyalin Sarkin Kano Sanusi na daya.
Allah Ya gafarta musu, Allah ya karbi bakuncinsu."
Kalli bidiyon jana'izar a kasa:
Takaitaccen bayani game da Sarki Sanusi I
Alhaji Sir Muhammadu Sanusi I, KBE, ya kasance mukaddashin Gwamnan Arewacin Najeriya a shekarar 1957, kuma Sarkin Kano daga 1954 zuwa 1963.

Asali: UGC
Shi ne ɗa na fari ga Sarkin Kano, Abdullahi Bayero, kamar yadda wata wallafa a shafin Wikipedia ta bayyana.

Kara karanta wannan
'Abin da ya sa Sarki Sanusi II bai halarci jana'izar Buhari ba da aka yi a Daura'
Sarki ne mai ƙarfi wanda ya kasance da tasiri sosai a Arewacin Najeriya a zamanin mulkin mallaka. Ya shirya babban bikin daba a lokacin da Sarauniya Elizabeth II ta kai ziyara Kano a 1956.
Rikicin siyasa tsakaninsa da ɗan uwansa, Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, da zarge-zargen almundahana sun kai ga tilasta masa sauka daga mulki, sannan ya koma zaman hijira a Azare a shekarar 1963.
Jikansa, Muhamadu Sanusi II, wanda ya rike mukamin gwamnan Babban Bankin Najeriya, ya zama Sarkin Kano daga 2014 zuwa 2020, kafin gwamnatin jihar ta sauke shi, sannan a sake mayar da shi a ranar 24 ga Mayu, 2024, karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Sanusi na daga cikin mabiya darikar Tijjaniyya da ke koyi da Ibrahim Niass kuma shi ma ya zama Khalifa.
Abin da ya hana Sanusi II zuwa jana'izar Buhari
A wani labarin, mun ruwaito cewa, an nemi sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II an rasa a wajen jana'izar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da aka yi a Daura.
Muhammadu Dallatu, makusancin sarkin Kano, ya shaida cewa Sanusi II yana halartar wani taro ne a London a lokacin, wanda shi ne dalilin rashin zuwansa Daura.
A cewar Dallatu, Sarki Sanusi II yana kasar Birtaniya ne kan wani aiki a hukumance kuma ana sa ran zai dawo Najeriya a ranar Laraba 16 ga watan Yulin 2025.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng