Yadda Sarki Sanusi I ya bar gadon sarauta a 1963
– Sarki Muhammadu Sanusi II ya tabo tsuliyar dodo kwanakin baya
– Wasu na ganin ana yi sauke sa daga kujerar a nada wani sabon Sarkin
– Haka dai aka yi wa Kakan sa a shekarar 1963
Idan ba ayi wasa ba za a iya sauke Sarkin Kano kamar yadda aka sauke Kakan sa.
Kujerar Sarki Sanusi II tana rawa bayan da aka shiga binciken fadar sa.
Haka aka yi da Kakan sa Sanusi I bayan ya samu matsala da masu mulki a lokacin sa.
An ce a wancan lokacin rikicin ya fara ne cikin gida bayan da daya daga cikin ‘Ya ‘yan Sarki Sanusi I ya saki matar sa wanda Diya ce wurin Sarkin Gwandu kuma ‘Yaruwar Sardauna. Sarkin ya kuma nemi ya ja da Sardaunan akan wasu dokoki da aka kafa.
KU KARANTA: Sarki Sanusi ya gargadi Shugabanni
A lokacin da aka yi dokar da ta karbe ikon filaye daga hannun Sarakuna dai Sarki Sanusi I bai ji dadin hakan ba. Wanda wannan ya kara jagwalgwala alakar su har ta kai aka tsige sa daga Sarautar inda ya koma Kasar Azare da zama.
Mun samu kishin-kishin kwakanaki cewa wasu daga cikin Gwamnonin Arewa sun yi wani taro game da Sarkin Kano a kasar China inda su ka nemi a tsige sa saboda irin cin fuskar da yake masu sai dai da alamu an sasanta Sarkin da Gwamnan Jihar Kano.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Muna cikin matsala a Najeriya
Asali: Legit.ng