Mata da yaran sarki Sanusi da aka tsige sun isa Awe

Mata da yaran sarki Sanusi da aka tsige sun isa Awe

- Matar tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ta isa garin Awe a jahar Nasarawa

- Jami'an DSS ne suka yi mata rakiya tare da yaran tsohn sarkin su uku

- Masu tsaron gidan sun bude masu sannan suka barsu suka shiga gidan da ake tsaron Sanusin

Daya daga cikin matan korarren Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ta isa garin Awe.

Ta isa garin da misalin karfe 11:15 na safe tare da yaran tsohon sarkin su uku, cikin wata mota kirar SUV fara mai bakin gilashi.

Jami’an yan sanda da na DSS be suka yi mata rakiya cikin motocin Hilux biyu dauke da lambobin motocin gwamnatin jahar Kaduna.

Mata da yaran sarki Sanusi da aka tsige sun isa Awe
Mata da yaran sarki Sanusi da aka tsige sun isa Awe
Asali: UGC

Jami’an tsaron da ke kan aiki ne suka bude masu kofa Sannan suka barsu suka shiga harabar gidan.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sarkin Awe, Alhaji Umar Isa Abubakar; shugaban Azara, Dr Kabir Musa Ibrahim da shugaban Aee, Alhaji Umar Da-Akani suna ganawa da korarren sarkin.

An kuma tattaro cewa kimanin jami’an tsaro 30 ne ke gadin gidan.

Ahalin da ake ciki, mun ji cewa korarren sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya dauki alwashin shigar da gwamnatin jahar Kano gaban kotu biyo bayan tsige shi da ya yi daga mukamin Sarautar Kano, tare da garkame shi.

Lauyan Sanusi, Abubakar Mahmoud SAN ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Talata, inda yace Sunusi ya basu umarnin kalubalantar tsige shi da aka yi, da kuma garkame shi da aka yi.

KU KARANTA KUMA: An tsaurara tsaro a sabon gidan Muhammadu Sanusi II da ke Awe

A cewar Mahmoud, garkame Sarki a wani wuri tare da hana shi walwala ba shi da asali a kundin tsarin mulkin Najeriya, don haka ya yi kira ga gwamnatin Kano ta sakan masa mara ya yi fitsari cikin sa’o’I 24 ko kuma ya kai shi kotu.

“Sakamakon umarnin tsohon Sarki ta hannun babban hadiminsa, ya bamu daman shigar da karar gwamnati gaban kotu domin kalubalantar tsige garkame shi tare da fatattakarsa daga garin Kano, muna da tabbacin hakan ya saba ma sashi na 35 na kundin tsarin mulkin Najeriya daya baiwa kowa daman walwala."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng