Yan Bindiga: Limami a Uromi da Aka Kashe Hausawa Ya Ƙaryata Rahoton Ƴan Sanda
- Babban limamin masallacin Juma'a na Uromi, Imam Muhammad Murtadha Obhakhobo ya karyata rahoton yan sanda
- Malamin ya ce ya biya N6.5m kudin fansa, ba 'yan sanda suka ceto shi ba daga hannun yan bindiga
- Limamin ya ce an sace shi ne a kan titin Ubiaja-Illushi ranar 9 ga Yuli, kuma an sako shi ranar 13 bayan an biya kudin fansa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Uromi, Edo - Babban limamin masallacin Juma’a na garin Uromi a jihar Edo, Imam Muhammad Murtadha Obhakhobo ya magantu bayan kubuta daga yan bindiga.
Malamin ya musanta ikirarin cewa ‘yan sanda ne suka ceto shi bayan sace shi da yan bindiga suka yi.

Source: Twitter
Rahoton Vanguard ya ce malamin ya bayyana cewa sai da ya biya N6.5m kafin yan bindigar suka sako shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da yan bindiga suka nema daga limamin
Legit Hausa ta ruwaito cewa an sace limamin ne a Uromi ranar 9 ga Yuli, inda masu garkuwar suka nemi a biya kudin fansa N30m.
Miyagun sun sace malamin ne jim kaɗan bayan da ya kammala sallar Azahar a ranar Lahadi 13 ga watan Yulin 2025.
Majiyoyi sun bayyana cewa tuni har sun kira iyalansa inda suka nemi a ba su maƙudan kuɗaɗen fansa.
Yan sanda sun ce sun ceto limami
Mai magana da yawun rundunar a Edo, CSP Moses Yamu, ya ce sun samu nasarar ceto limamin bayan matsin lamba da suka rika yi.
Hakan ya sa limamin fayyace gaskiyar abin da ya faru sabanin abin da yan sanda suka ce a cikin wata sanarwa, cewar The Guardian.
Amma a lokacin wata tattaunawa da manema labarai, limamin ya ce akasin hakan ne, domin kuwa sai da ya biya kudin fansa kafin a sako shi.
Ya ce:
“Ni ne Imam Muhammad Murtadha Obhakhobo, babban limamin masallacin Juma’a na Uromi a Edo an sace ni ranar 9 ga Yuli, 2025 a kan titin Ubiaja-Illushi.
“Na kubuta ne bayan na biya Naira miliyan 6.5 ranar 13 ga Yuli, amma sai na ji a labarai cewa wai ‘yan sanda ne suka cece ni."

Source: Facebook
Yan bindiga: Limami ya soki azarbabin yan sanda
Limamin ya ce bayan dawowarsa daga hannun masu garkuwa, shugaban sashen ‘yan sanda na Uromi ya ziyarce shi domin jin bayani, wanda ya ba su.
Ya ce bayan ya bayyana wa DPO yadda abin ya faru, sai kawai ya ga ‘yan sanda na neman daukar lamban yabo ba tare da sun yi komai ba.
“An sako ni ne sakamakon kokari na kaina da kuma biyan kudin fansa mai yawa, ba wai saboda kokarin ‘yan sanda ba."
- In ji limamin
Sai dai ya bayyana godiyarsa ga duk wadanda suka yi addu’a da nuna damuwa a lokacin da yake hannun masu garkuwa da mutane.
Yan bindiga sun sace limami a Zamfara
Mun ba ku labarin cewa an tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun sace babban limamin masallacin Juma’a na Faru, Imam Sulaiman Idris da ke karamar hukumar Maradun a Zamfara.
Majiyoyi sun nuna cewa an kama limamin ne da safiya yayin da yake aiki a gonarsa, kuma har yanzu ba a san inda yake ba.
Wani rahoto ya nuna cewa mazauna garin sun bayyana fargaba da fushi, suna kira ga hukumomin tsaro da su dauki mataki cikin gaggawa.
Asali: Legit.ng


