Yadda aka Yi Jimamin Rasuwar Shugaba Buhari a Jihohin Arewa
- Arewacin Najeriya na cikin alhini yayin da aka yi jana’izar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura
- Malamai da jama’a sun gudanar da addu’o’i a Gombe, Yobe, Bauchi da sauran jihohi domin neman rahamar Allah ga Buhari
- Shugabannin addini da sarakuna sun bayyana shugaba Muhammadu Buhari a matsayin shugaba mai gaskiya da sadaukarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina – Lokacin da aka birne Muhammadu Buhari a Daura ranar Talata, dukkan yankin Arewacin Najeriya ya rude cikin jimami da alhini.
Tsohon shugaban kasar ya rasu ne ranar Lahadi a wani asibiti da ke London, kuma mutuwarsa ta girgiza al’umma da dama musamman a Arewa inda aka gudanar da taruka na musamman.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta hada rahoto kan yadda aka yi jimamin rashin shugaba Buhari a jihohin Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan
UNIMAID: An faɗi babban dalilin da ya sa Tinubu ya sauya sunan jami'a saboda Buhari
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarakuna da dagatai daga Katsina, Kano, Gombe, Sokoto, Zaria, Borno da Bauchi sun yi kasa da tutoci a matsayin alamar girmamawa, yayin da aka gayyaci malamai domin gudanar da addu’o’i.
An yi wa Buhari addu’a a Gombe da Yobe
Legit ta rahoto cewa, jihar Gombe, jama’a da malamai sun gudanar da Salatul Gha’ib – sallar jana’iza daga nesa – a kusa da filin wasa na Pantami.
Rahotanni sun nuna cewa daruruwan jama’a sun taru domin yin addu’a ga Muhammadu Buhari da neman gafarar Allah a gare shi.
A Yobe kuwa, Gwamna Mai Mala Buni ya umurci limamai da su jagoranci addu’a a masallatai da fadar sarki.

Source: Facebook
Limamin masallacin jami’ar Yobe, Ustaz Hamza, da sauran malamai a Damaturu sun ce Buhari ya mutu ne yana mai kishin kasa da riko da gaskiya.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa an yi sallar gawa daga nesa wa shugaba Muhammadu Buhari a jihar Filato.

Kara karanta wannan
Malaman Musulunci da Kiristoci sun taru a Daura, an hadu don roka wa Buhari rahama
Bauchi da Borno sun yi alhinin Buhari
A jihar Bauchi, makarantar Madarasatu Tarbiyatul Aɗafal Wa Tahfizil Qur’an Kareem ta gudanar da addu’o’i na musamman tun ranar Litinin.
Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban makarantar, Malam Abdullahi Hashimu ne bayyana hakan ga manema labarai.
Malamin ya ce:
“Mun fahimci cewa mu talakawa ba mu da wani abin da za mu yi sai addu’a.”
Malam Abdullahi Hashimu ya kuma bukaci sauran makarantu su yi haka domin samun lada da rokon Allah ya jikan Buhari.
A Borno kuwa, tituna sun yi shiru, shaguna da dama sun rufe, yayin da mutane ke jimamin rasuwar Buhari.
An yi jimamin rashin Buhari a Kaduna
A jihar Kaduna, tashar Freedom Radio ta gabatar da shirin musamman mai taken “Buhari: Rayuwarsa da Kadan daga Abubuwan da Ya Bari,”
Rahotanni sun bayyana cewa mutane suka kira suna bayyana shi a matsayin “uban Arewa” da “mai kare talakawa.”
Shugaban kungiyar dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi, ya bayyana Buhari a matsayin jagora da ya tsaya tsayin daka wajen kare mutuncin Arewa.

Kara karanta wannan
Hoton yadda Aisha Buhari ta rungume tutar da aka lulluɓo gawar mijinta ya ja hankali
Ya ce:
“Ko da yake Buhari mutum ne kamar kowa, yana da kura-kurai, amma kishi da kwazon sa ba su da misaltuwa.”
Kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen Arewa ta bayyana Buhari a matsayin “uba ga kowa” wanda ya bar tarihi mai kyau a Najeriya.
Shugaban kungiyar, Fasto Joseph Hayab, ya ce:
“Ko da mun saba da ra’ayinsa a wasu lokuta, ba mu taɓa shakkar gaskiyarsa ba. Najeriya ta yi babban rashi.”
Legit ta tattauna da Hamza Ibrahim
Wani matashi a jihar Gombe, Hamza Ibrahim ya ce shi ma yana yi wa Buhari addu'ar samun gafarar Allah.
"Sai dai duk da haka ba na ganin ya kamata a ce wai dole sai mutane sun yafe masa abubuwan da ya yi.
"A ra'ayina, hakan bai dace ba, bai kamata malamai su rika tilasta mutane su yafe wa Buhari ba."
An nemi Tinubu ya kara girmama Buhari
A wani rahoton, kun ji cewa an bukaci shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya kara girmama Muhammadu Buhari.
Wani jigon APC, Dr Aliyu Ibrahim ne ya bayyana haka jim kadan bayan an kammala jana'izar Buhari a Daura.
Dr Aliyu ya roki shugaba Bola Tinubu da ya sanya sunan Muhammadu Buhari a wasu manyan cibiyoyin gwamnati a kasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
