Iyalai na Hawaye, Shugaba Tinubu Ya Karɓi Gawar Muhammadu Buhari a Katsina
- Bayan isowar tawagar Kashim Shettima, Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya karɓi gawar Marigayi Muhammadu Buhari a Katsina
- Tinubu ya karɓi gawar ne a gaban manyan ƙusoshin gwamnati da iyalan mamacin, wanda idanunsu ke ci gaba da zubar da hawayen jimami
- Gwamna Dikko Raɗɗa da wasu daga cikin gwamnonin jihohin Najeriya, ministoci da ƴan kasuwa sun halarci wurin karɓar gawar Buhari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya karɓi gawar magabacinsa, Alhaji Muhammadu Buhari, wanda Allah ya yi wa rasuwar ranar Lahadi da ta gabata a Landan.
Shugaba Tinubu ya karɓi gawar ne daga tawagar gwamnatin Najeriya ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima bayan sun iso Katsina.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Shettima da wasu daga cikin iyalan Buhari ne suka yiwa gawar rakiya tun daga Landan zuwa jihar Katsina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu ya karbi gawar Buhari
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru da manyan kusoshin gwamnati da iyalan mamacin na tsaye a filim jirgin lokacin da Shugaba Tinubu ya karɓi gawar Buhari.
A yau Talata, 15 ga watan Yuli, 2025 za a yi wa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari jana'iza tare da birne shi a cikin gidansa da ke garin Daura.
A wani bidiyo da Imran Muhammeɗ ya wallafa a X, an ga lokacin da aka sauko da gawar Buhari daga cikin jirgi yayin da iyalai ke zubda hawayen da jimamin rashin.
Gwamnoni da jiga-jigan da suka halarci wurin
Daga cikin waɗanda suka halarci filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa domin karɓar gawar Buhari har da Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun.
Haka kuma wasu gwamnoni daga jihohin ƙasar sun halarta, ciki har da:
1. AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara
2. Mai Mala Buni na Yobe
3. Muhammadu Inuwa Yahaya na Gombe
4. Umar Namadi na Jigawa
5. Nasir Idris na Kebbi
6. Dauda Lawal na Zamfara
7. Ahmed Aliyu na Sokoto
8. Babajide Sanwo-Olu na Legas
9. Dapo Abiodun na Ogun
10. Monday Okpebholo na Edo
11. Hope Uzodimma na Imo
12. Bassey Edet Otu na Cross River.
Daga jihar mai masaukin baki, mataimakin gwamna Faruk Lawal Jobe; Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura sun halarci tarbar gawar Buhari.
Hadimin Shugaban Ƙasa, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro da ministoci da manyan jami'ai suna wurin.
Tawagar gwamnatin Nijar ta iso Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Firaministan Jamhuriyar Nejar da tawagarsa sun iso Najeriya domin halartar jana'izar Muhammadu Buhari a Daura.
Ana sa ran shugabannin kasashen Chadi, Gambiya da Guinea Bissau za su shigo Daura domin halartar jana’izar tsohon shugaban Najeriya.
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Raɗɗa da wasu daga cikin ƴan kwamitin shirya jana'izar ne suka tarbi tawagar gwamnatin Nijar a filin jirgin sama yau Talata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
