Bidiyo: Cikin Hawaye, Fatima Buhari Ta Isa Daura inda Za a Binne Gawar Mahaifinta

Bidiyo: Cikin Hawaye, Fatima Buhari Ta Isa Daura inda Za a Binne Gawar Mahaifinta

  • An ga Fatima Buhari, 'yar marigayi Muhammadu Buhari, ta isa gidansu a Daura cikin hawaye yayin da ake shirin jana'izar mahaifinta
  • An sanar da cewa jirgin sojin sama ya ɗauko gawar marigayi Shugaba Buhari daga Landan zuwa Katsina don a binne shi a garinsa na Daura
  • Bidiyon da Legit Hausa ta samu ya nuna Zahra da wasu daga cikin 'yan uwansu suna zubar da hawaye yayin da ake kokarin rarrashinta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Daura - 'Yar fari ga marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Fatima (Magajiya) Buhari, ta isa gidan mahaifinta a Daura ranar Talata cikin kuka, yayin da iyalan ke shirin jana'izarsa.

Fatima ta yi matukar baƙin ciki da wannan rashi, kuma an gan ta tana kuka a hankali yayin da abokai da 'yan uwa na kusa ke rarrashinta.

Kara karanta wannan

An yi wa Buhari sallar jana'iza a Gombe yayin da ake jiran gawar shi a Daura

Fatima ta fashe da kuka da ta isa gidansu na Daura inda za a binne gawar Buhari
Fatima tana zubar da hawaye a gidansu na Daura, inda za a rufe tsohon shugaban kasa Buhari. Hoto: @SarkiAbdulwahab
Source: Twitter

Sauran 'yan uwan marigayin ma sun fara isowa gidan na Daura da safiyar Talata, tun ma kafin gawar tsohon shugaban ya iso Najeriya daga Landan, inji rahoton The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigilar gawar Buhari daga Landan

Tun da sanyin safiyar yau, gawar marigayi shugaban ta bar Landan a cikin jirgin saman sojin saman Najeriya, inda take kan hanyarta ta zuwa Katsina don binne shi a garinsu na Daura.

A halin da ake ciki, uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bar Abuja kuma tana kan hanyarta ta zuwa Daura don halartar jana'izar.

Har ila yau, kwamitin mutane 25 da Shugaba Bola Tinubu ya kafa don shirya jana'izar Buhari ta kasa, ya iso jihar Katsina.

Kwamitin, wanda sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, ke jagoranta, yana aiki tare da gwamnatin jihar Katsina da iyalan Buhari don tabbatar da cewa an gudanar da jana'izar cikin mutunci da tsari.

Kara karanta wannan

An gano bidiyon Aisha Buhari tana rusa kuka a gaban Shettima yayin da ya ke ta'aziyya

Tsohon shugaba Muhammadu Buhari ya yi shugabancin na sau uku a lokuta daban daban.
Muhammadu Buhari, a lokacin da zai hau jirgin sama, lokacin yana shugaban Najeriya. Hoto: @BashirAhmaad
Source: Facebook

Rayuwar Buhari da shirye-shiryen gwamnati

Buhari ya rasu ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin 2025 a wani asibiti a Landan bayan doguwar jinya, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Ya yi aiki a matsayin shugaban mulkin soja daga 1983 zuwa 1985, sannan daga baya a matsayin zababben shugaban kasa daga 2015 zuwa 2023.

Mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta ayyana jana'izar kasa baki daya don girmama shi, kuma ta sanar da ranar Talata, 15 ga Yuli, a matsayin ranar hutu.

An ayyana zaman makoki na kasa na tsawon kwana bakwai, inda za a sauke dukkan tutoci zuwa rabin sanda a fadin kasar da kuma a ofisoshin jakadancin Najeriya a kasashen waje.

Ministan labarai, Mohammed Idris, ya kuma sanar da cewa an buɗe littattafan ta'aziyya a dukkan ma'aikatun tarayya, hukumomi, ofisoshin jakadancin Najeriya, da kuma babban dakin taro na kasa na Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Mutanen Daura sun fadi yadda Buhari ya rayu a tsakaninsu bayan sauka a mulki

Kalli bidiyon Fatima Buhari a nan kasa kamar yadda TVC News ta rahoto:

Zahra tana kuka a asibitin da Buhari ya rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, iyalan tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na cikin tsananin jimami bayan tabbatar da rasuwarsa a wani asibiti da ke Landan.

Wani faifan bidiyo ya nuna Zahra Buhari tana kuka a gaban asibitin, yayin da sauran 'yan uwanta ke rike da ita suna rarrashinta.

An ruwaito cewa manyan jami'an gwamnati da tsofaffin shugabannin kasa, kamar Abdulsalami Abubakar da Rochas Okorocha, sun kai ziyara asibitin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com