Gwamnatin Tarayya Ta Bude Shafin Daukar Matasa Marasa Aiki a Najeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Bude Shafin Daukar Matasa Marasa Aiki a Najeriya

  • An buɗe shafin daukar aiki a Najeriya a yau Litinin, 14 ga Yuli 2025, domin daukar sababbin ma’aikata a hukumomi daban daban
  • Za a dauki ’yan Najeriya maza da mata masu shekaru tsakanin 18 zuwa 35 waɗanda ke da cikakken lafiya kuma suka cancanta
  • Gwamnatin Tarayya ta ce za a ɗauki sababbin jami’ai 30,000 a hukumomin tsaro na NSCDC, hukumar kashe gobara da sauransu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta buɗe shafin neman aiki domin daukar sababbin ma’aikata a hukumomi hudu.

Za a dauki ma'aikata ne a hukumar shige da fice, hukumar tsaron hararen tula ta NSCDC, hukumar kashe gobara, da kuma hukumar gidajen gyaran hali.

Za a dauki ma'aiakata 30,000 a Najeriya
An fara daukar ma'aikata 30,000 a Najeriya. Hoto: Imran Muhammad
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa an sanar da hakan ne ta hannun hukumar gudanarwar waɗannan hukumomi wato CDCFIB a wata takarda da ta fitar tun a watan Yuni.

Kara karanta wannan

Tarihi da muhimman abubuwa game da marigayi shugaba Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sharuddan nema da yadda ake cike form

An shirya fara ɗaukar aikin tun a ranar 26 ga Yuni, amma daga bisani aka dage zuwa yau Litinin, 14 ga Yuli 2025 saboda wasu dalilai.

Shafin da ake amfani da shi wajen cike takardun neman aikin shi ne a nan, kuma an shawarci masu sha’awar aikin su karanta cikakkun bayanai da ke shafin kafin su nema.

Ma’aikatar ta bayyana cewa ana bukatar ’yan Najeriya maza da mata, masu shekaru tsakanin 18 zuwa 35, waɗanda ke da cikakken lafiya ta jiki da hankali.

An kuma bukaci masu sha’awa su bi doka da oda wajen neman aikin tare da guje wa saka bayanan bogi.

Ana sa ran ɗaukar jami’ai 30,000 a hukumomi

Bayanin daukar aikin ya fito ne daga wata sanarwa da gwamnatin tarayya ta fitar a watan Yuni, inda ta bayyana shirinta na daukar ma’aikata 30,000 domin cike gibin da ke hukumomin.

Kara karanta wannan

NiMet: Za a sha ruwa da tsawa a Kano, Yobe da jihohin Arewa 13 a ranar Lahadi

Matakin yana daga cikin kokarin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na rage rashin aikin yi da inganta tsaro a Najeriya baki ɗaya.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Za a raba sababbin jami’an da za a ɗauka zuwa sassa daban-daban na ƙasar domin yin aiki da waɗannan hukumomi.

Matasa na nuna sha’awar naman aikin

Rahoton The Guardian ya nuna cewa mutane da dama sun shiga shafin neman aikin tun daga safiyar yau Litinin, inda aka tabbatar da cewar shafin ya fara aiki da misalin ƙarfe 11:30 na safe.

Wasu matasa sun bayyana farin cikinsu da wannan dama, inda suka ce lokaci ne da gwamnatin tarayya ta bai wa jama’a damar samun aiki ba tare da son rai ba.

Dangote zai dauki matasan Najeriya aiki

A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya sanar da shirin daukar matasa aikin wucin gadi a kamfanin shi.

Sanarwar da kamfanin Dangote ya fitar ta nuna cewa za a dauki matasan aiki ne domin ba su horo a fannoni.

Dangote ya kafa sharadin cewa dole matashin da za a dauka ya zamo ya kamma digiri ko matakin HND kuma ya mallaki shaidar hidimar kasa ta NYSC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng