Rai Bakon Duniya: Basarake Mai Daraja a Najeriya Ya Koma ga Mahaliccinsa
- Jihar Delta ta yi rashi na ɗaya daga cikin manyan sarakunan da ake ji da su bayan mai martaba Uhurhie-Osadere II ya koma ga mahaliccinsa
- Sarkin na masarautar Olomu mai daɗaɗɗen tarihi ya yi bankwana da duniya ne shekara biyu bayan ya ɗare kan kujerar da ya gada wajen kakanninsa
- Rasuwarsa ta sanya an ayyana zaman makoki na wata guda tare da rufe kasuwanni a masarautar Olomu da ke ƙaramar hukumar Ughelli ta Kuɗu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Delta - An shiga jimami a jihar Delta bayan rasuwar mai martaba Ohworode na masarautar Olomu mai tarihi, Uhurhie-Osadjere II.
Mai martaba Uhurhie-Osadere dai yana sarauta ne a masarautar Olomu da ke ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.

Source: Facebook
An sanar da rasuwar basaraken ne a hukumance a fadar sarkin da ke ƙauyen Ovwor-Olomu cikin masarautar, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Basarake ya rasu a jihar Delta
Otota na masarautar, Olorogun Albert Akpomudje (SAN), tare da ƴan majalisar sarakunan gargajiya na Olomu da kuma ƴan uwan marigayin, ne suka sanar da rasuwar a hukumance.
Rasuwar tasa ta faru ne shekaru biyu bayan ya hau karagar sarauta ta kakanninsa a ranar 20 ga watan Mayu, 2023.
Sanarwar ta kasance tare da harba bindiga har sau 21 a matsayin girmamawa da kuma rawar gargajiya daga ƴan rawa na Ema.
Biyo bayan wannan sanarwa, duk kasuwanni a cikin masarautar za a rufe su, sai dai za a ba shaguna damar yin mu’amala ta cinikayya ƴar kaɗan.
Haka kuma, an dakatar da gudanar da jana’iza da bukukuwan aure yayin da masarautar ta shiga zaman makoki.
Masarautar ta ayyana wata guda na zaman makoki daga ranar Asabar, 12 ga watan Yuli, zuwa 12 ga watan Agusta, 2025.
An umarci sarakunan gargajiya na masarautar Olomu da su ɗaura igiyar makoki a hannun hagu tare da kin saka hular ja ta sarautar gargajiya ta Olomu a matsayin girmamawa ga marigayi sarkin.

Kara karanta wannan
'Yan Najeriya sun fara nuna wanda suke so jam'iyyar haɗaka ADC ta tsayar takara a 2027

Source: Original
Karanta wasu labaran kan rasuwar rashe-rashe
- Bayan rikici kan nadinsa, basarake ya rasu watanni kadan da karbar sarauta
- Mutuwa mai yankan kauna: Fitaccen basarake ya rasu, Tinubu ya jajantawa al'umma
- Innalillahi: Babban basarake ya rasu jim kadan bayan dawowa daga Sallar Idi
- Ana tsaka da rigimar sarauta a Kano, fitaccen basarake ya mutu a Arewa
- Fitaccen basarake a Najeriya ya kwanta dama, gwamna ya nuna alhini
- Lokaci ya yi: Tsohon mataimakin gwamna a Najeriya ya rasu
- Cashman: Shugaban ƴan fim ya rasu, Ali Nuhu da sauran jarumai sun yi jimami
Mahaifin tsohon gwamna ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Allah ya yi wa mahaifin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero rasuwa.
Marigayi Alhaji Ramalan Yero wanda ke riƙe da sarautar Turakin Dawakin Zazzau ya yi bankwana da duniya ne a ranar, 12 ga watan Mayun shekarar 2025.
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya aika da saƙon ta'aziyyarsa kan rasuwar marigayin, wanda ya bayyana a matsayin mutum mai kyawawan halaye.
Asali: Legit.ng
