Ba Da’a: Hankula Sun Tashi da Dalibin Sakandare Ya Yiwa Malami Duka Har Lahira

Ba Da’a: Hankula Sun Tashi da Dalibin Sakandare Ya Yiwa Malami Duka Har Lahira

  • Wani ɗalibi mai shekara 16 daga JSS3 ya halaka malaminsa a Oju, Jihar Benue, bayan faɗa kan hular makaranta da aka ce an kwace daga dalibin
  • An ce ɗalibin, Friday Ogamude, ya kai wa Malam Oyibe Oyibe duka yayin cece-kuce, inda malamin ya faɗi ƙasa ya mutu yayin da aka kai shi asibiti
  • Rundunar ƴan sanda ta cafke wanda ake zargi, ta ce za a tabbatar da adalci yayin da bincike ke ci gaba da gudana a lamarin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Makurdi, Benue - Wani mummunan lamari ya faru a jihar Benue bayan wani dalibi ya hallaka malaminsa da duka wanda ya tayar da hankulan mutane.

Lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Oju ta Jihar Benue ranar Alhamis 10 ga watan Yulin 2025 lokacin da ake tsaka da karatu da karatu a makarantar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya wanke Fulani, ya fadi masu kai hare hare a jiharsa

Dalibi ya hallaka malaminsa da duka a Benue
Yan sanda sun kama dalibi da ya kashe malaminsa. Hoto: Fr. Alia Hyacinth.
Source: Twitter

Dalibi ya yi ajalin malaminsa a Benue

Rahoton Zagazola Makama ya ce ɗalibin wanda ke matakin JSS3 ya kashe malaminsa saboda hularsa da aka kwace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi sun shaida cewa wanda ake zargin mai suna Friday Ogamude, ɗalibi mai shekara 16 na makarantar UBE Oju Centre ne.

An ce Friday Ogamude ya yi wa malaminsa, Mr. Oyibe Oyibe mai shekara 35, barazana bisa wata hula da malamin ya karɓa tun watan Mayu 2025.

A cewar majiyoyin, cece-kuce ya rikide zuwa faɗa yayin da ɗalibin ya kai wa malamin duka, inda aka ce malamin ya zube nan take.

An kama dalibin da ya kashe malami a Benue
Dalibi ya yi sanadin malaminsa a jihar Benue. Legit.
Source: Original

Matakin da yan sanda suka dauka kan dalibin

An garzaya da shi zuwa asibitin Amara da ke Oju, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa bayan gwaje-gwaje da aka gudanar, cewar The Guardian.

An dauki hoton gawar mamacin sannan aka ajiye ta a Asibitin Gwamnati da ke Oju domin gudanar da bincike.

Kara karanta wannan

JAMB ta saki bayanan dalibin da ya fi kowa samun maki a jarabawar UTME 2025

Jami’an ‘yan sanda sun ce sun cafke wanda ake zargi, kuma rundunar ta la’anci lamarin tare da tabbatar da cewa za a hukunta mai laifi.

Ana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin domin gano cikakken gaskiyar yadda lamarin ya faru da kuma dalilan dake bayansa.

Legit Hausa ta tattauna da wani malami

Wani kwararren malamin makaranta, Yakubu Muhammad ya ce dole malamai su yi taka tsan-tsan wurin mu'amala da dalibai.

Ya ce abin da dalibin ya yi abin takaici ne ko ba komai malami yana da daraja fiye da komai domin shi ne silar samun ilimi.

Ya ce:

"Wanna abin takaic ne gaskiya, ya kamata malamai su san yadda suke mu'amala da dalibai saboda mafi yawansu ba su da tarbiya musamman a makarantun gwamnati."

Ya shawarci gwamnati da makarantu masu zaman kansu su inganta albashin malamai domin yana kara raini a tsakaninsu da dalibai.

Daliba ta yi niyyar sare kan malami a Kano

Mun ba ku labarin cewa wata daliba a Kwalejin Polytechnic ta Kano tare da saurayinta sun kai hari kan wani malami a Kwalejin fasahar.

Kara karanta wannan

Atiku ya tabo batun takara a 2027, ya fadi abin da zai yiwa yan Najeriya

A cewar hukumar makarantar, saurayin dalibar ya yi yunkurin sare kan malamin a cikin ofishin da ke kwalejin.

Jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin cafke dalibar da saurayinta a unguwar Dorayi, amma 'yan daba sun dakile yunkurin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.